Book
a makabarta aka haifeni
By Fatima Omar
   

About this book


Babban mutum ne, kuma kyakkyawan dattijo wanda akalla baze wuce shekaru 50 aduniya ba, acikin keken guragu aka turoshi wanda da alama yana fama da mutuwar shanyewar barin jiki, daga dakin gashi aka fito dashi bayan angama gasa mashi jikinshi, wanda ake masa duk bayan kwana 3. Sarki Qaseem ne yashigo dakin wanda yakasance kanine ga dattijon dayake bisa kujera. Sannu Yaya yakarfin jikin? Kwalla ce tacika idonshi, wadda tariga da tazamar mashi sabo aduk lokacin dazeyi magana, Babban bawan dayake kusa dashi wanda yazama shine hadiminshi yasaka kyalle yayi saurin goge mashi idonshi. Hannu Sarki Qaseem yadaga, nan take kowa yabar dakin. Zama yayi kusa dashi yadafa kafarshi, fuskarshi cike da damuwa, yace Yaya dan Allah kayi hkr, yakamata ace zuwa yanzu kayi hkr da abinda yafaru shekaru 18 dasuka wuce. Akullum semunsa manyan malamai sunyi addu,a akan damuwar datake cikin masarautar nan. Kuma kasan ba,a fidda rai da rahamar Ubangiji. Murmushi yayi tare da girgiza kai, yana kallon kaninnashi, wanda yake so sosai, kasancewar shikadai gareshi kuma Uwa daya Uba daya suke. Sarki Qaseem shima murmushin yayi ganin Yayanshi yanayi, yace tabbas Yaya yau naji dadin ganin murmushi afuskarka, wanda rabon dakayi hakan tunkafin karasa farincikinka. Segashi yau kayimun murmushi. Dariya ce tafito daga cikin dakin, wanda wasu manyan mata ne, zaune acikinshi. Daya daga ciki tace, ai wlh Medaki kema kinsan bazan taba barin aci mana fuska acikin gidan sarauta ba, kamar yanda kikazo kika sameni acikin gidan nan shekarata nawa kika sani muna tare da Memartaba, kuma nayi hkrn zama dashi, harkikazo kika sameni, kekanki dabakiyi biyayya ba, ai da tuni nayankar maki Ticket nabarin duniyar baki daya... Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review