Book
baqin aljani
By Fatima Omar
   

About this book


Ganin suna nufota yasa ta fadi 'kasa su mamma, ta farka ta ganta a dakinta duk jikinta na mata ciwo ga bakinta na mata wani azaban zafi, taga khausar kusa da ita tana kuka, da sauri Hajiya ta tashi tayi bayi taga bakinta yayi mugun kumbura, ta fito khausar ta bita da kallo sannan tace mumy maiya sameki na tashi na ganki a dakina a kwance a 'kasa ina ta tashinki kinki ki tashi saida na kira Dr yace min wai akwai abunda ya harbeki, shine ya miki allura, Hajiya da ta kura ma khausar ido, babu abunda takeyi sai hawaye, maike faruwa ne? Khausar ce ta katse mata tunani da fadin mumy maiya harbeki? Hajiya dake hawaye tace niba ban San ko miye bane khausar, nan dai khausar din tayi shiru, Hajiya ta aiyana a ranta tabbas ya kamata ta kira barrister salman ya dawo domin yasan abunda ake ciki, jin khausar din tayi tana dariya mai karfi tare da wani murya mai kaman na kuturu ta fara magana,"Hajiya wannan Kadan kika gani khausar tawa ce, saina azabtar dake kaman yanda nima kika min. Hajiya dake kan gado bata San sanda ta sauko tayo kasa ba, duk ta fita hayyacinta, jin khausar din tayi tana cewa mumy maiya sameki? Hajiya ta fashe da kuka tana fadin khausar tashi kije dakinki dan Allah, wani uban dariya khausar din ta kuma saki mai ban tsoro, tace hajiya kina da iko da khausar amma bamu ba, haka zaki kasance cikin kunci kaman yanda kika samu, hajiya ta kudun dune waje daya kukan ma yanzu ta kasa yi saboda tsoro, idon khausar taga yana canzawa yana komawa green ta kuma tsorata, wata iska ta gani yazo yayi sama da ita, tun daka lokacin bata kuma Sanin inda kanta yake ba, tadai farka ta ganta a cikin wani daji an daureta ga khausar nan tana ta rawa da kuma karan kida da take ji, duk ta tsorata can taga wata mai kama da khausar itama tazo, wata ta kuma zuwa, masu kama da khausar suka cika wajan baza ma ka gane wacece aini yin khausar din ba, sai rawa sukeyi kaman macizai, ga kidin da akeyi ba dadin ji, hajiya tayi mugun fita hayyacinta ji tayi kaman ana zaneta da bulala ta fara ihu tana fadin duk addu'an daya fado bakinta, lokaci daya aka tsaya da dukan, wani hayaki ta gani taga khausar a ciki tasa wani kaya na alfarma akan wani Kujera, tana dariya mai karfi, ta fara magana cikin wani yare, lokaci daya saiga wasu hallita sun fara bayyana mai ban tsoro, dukan su suna da kaho a Kansu sannan fuskansu sak irin na tsuntsu jikinsu irin na mutane, suna sanye da wani bakin yadi a jikinsu, suka fara nufota duk addu'an daya fado mata yi takeyi saida suka zo daf da ita, suka tsaya jin wani kara tayi mai razanarwa tun daka lokacin bata san inda kanta yake ba, tadai farka taganta a kwance a gadon asibiti, ga kuma babban danta dake gefe sai Barrister salman dake kusa Dashi, ganin ta farka da sauri ashraf ya fita kiran Dr, bai jima da fita ba saiga suka dawo tare da Dr, hajiya hawaye ke zuba a idonta domin tana tausayin Yar tata, amma yanzu tunda barrister yazo da dan sauki, Dr ya mata sannu da jiki sannan ya mata tambayoyi, yace ta rage yawan tunani domin jininta ya hau sosai, hajiya tace a sallameta ta koma gida, aiko haka akayi aka bata takardan sallama, suka nufi gida, alokacin da suka Shiga falo khausar ta fito cikin wani riga da wando ya kamata sai kamshin turare takeyi, barrister salman da tun shigowarsu ya kura mata ido cike... Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review