BUGUN ZUCIYA
Title: BUGUN ZUCIYA
Author: Ash24
Category: Romance
Language: Hausa
Price: ₦ 500
No. of Words: 103324
Rating:
Your Rating:
Downloads: 10
Tags:
  • Hausa
  • Novels
  • Soyayya
  • Ash24

Description:
Turbune fuska yariyar tayi lokacin da sukayi ido biyu da kakar tata tana fadin ayya dada danma kinsamu ina murnan ganinki shine zakice wani kin shigesu?, juyawa tayi da nufin komawa, cikin sauri dada ta jawota cikin fara'a tace dawo2 ai ban dauki murya ba, maraba lale lale takwara, karashewa tayi tare da jawota jikinta ta rungume" Daidai lokacin wani farin dattiju ya shigo tare da sallama, yana ganin su haka yasaki murmushi" Cikin sauri yariyar ta kwace daga rukon dada ta nufi cikin dakin, tabarma ta dauko ta shinfida wa mahaifinta ya zauna tana jin sun shiga gaisawa da dada ta koma dakin dada" Gyarawa tashigayi duk da cewa dakin agyare yake dan dada macece me matukar tsafta, gadon ta lokuikuye yayi tsaf kaman baza ahauba sannan ta dau tsintsiya tahau shara" Bayan ta gama ne ta dauko dan kaskon turaren wuta ta nufin dan karamin kitchen din dada dake tsakar gida" Tagabansu dada tazo zata wuce dan haka duk suka juyo suna kallonta harta kusa isa kitchen din dada tace" Aiko takwara bazaki samu rushi a kitchen dinnan ba, dan yanzun baban ninki sun hanani amfani da murhu" Juyowa tayi ahankali tace to yanzun baki kunne turaran rushi kenan? Gurin tabawa nake samowa" Cikin rawar jiki ta nufi kofar gida tana fadin bari naje na samo" Lokacin da dada ta komar da kallonta ga dannata gani tayi yayi shiru kanshi akasa, gyaran murya tayi sannan tace girman dan mutum babu wuya yanzun dan Allah kalli yadda takwara ta girma ko yanzun aka mata aure saita xauna" Da sauri ya dago kai, yace dada kin sosamin inda ke min kyaikayi, hankalina ya fara tashi ayau tum muna hanya zuciyata ta fara tsinkewa" Cikin kulawa tace kakwatar da hankalin ka insha Allahu Allah zai tsare babu abin da zai faru, kuma ma ai takwarar tawa Allahamdulillahi natse take tsaf ga kunya ga tsafta" Hmmm dada akwai wani hali dana kula tanashi wadda har yanzun banji kowa ya furta ba, ban saniba koni kadai nake gani?
Share book:
Buy

Comments (0)