Book
ciki da gaskiya
By Abbas Abari
   

About this book


Falon yayi shiru, kowa ya maida hankalinsa ga baffah, dukda ba wannan ne karon farko da aka ta6a irin wannan taronba agidan kuwa. Amma a wannan karon sai taron yafirgita zuciyar wasu daga cikin al'ummar gidan, musamman ma hajia babba da gwaggo bintu, Dan taron harda su Aysha aciki, da ita kanta gwaggo bintun. Bayan an bud'e taro da addu'oi Ammah tafara magana. Nasan zakuyi mamakin wannan taro, to kudaina mamaki, nice nasaka babanku yayishi, maganar gsky taron yashafi wasunku, kuma ina fata yazama alkairi agaremu baki d'aya. Ta maida kallonta ga baffah, tareda jinjina masa kai, alamar tabar wuk'a da nama a hannunsa. Baffah yafara da sallama da nasiha, sannan yad'ora da fad'in wannan zama yashafi 6angarorine guda biyu zuwa uku. Na farko shine bintu wadda kuke kira Maman yara tanada alak'a ga fad'ima, nasan kuma duk kunsan haka. Duk suka amsa da eh. To alhmdllh, daga yanzun tafita daga jerin masu aikin gidannan, itama tadawo cikinmu, zata cigaba da zama wajen fad'ima insha ALLAH. Kowa ya nuna farincikinsa, Dan bazasu iya manta alkairin gwaggo bintu ba akan d'awauniyar yaran gidan, tundaga kan Amatullah taketa d'awainiya dasu, wannan yasaka taci suna Maman yara. Ayanda nakula hajia babba ce kawai batayi na'am da batunba, amma batace uffanba. Baffah yaciga da fad'in, akwai yarinyar Hama maisuna bishirah, zatayi aure nanda 2 month's idan ALLAH ya kaimu, to tunda bikinta yataho, itama mun dakatar da ita ta huta, ALLAH ya Sanya alkairi. Nanma akace amin. 6angare na biyu kuma shine, za'a kawo sabbin masu aiki su hud'u insha ALLAH, dansu zama canji gasu bintu d'in. Kashi Na uku kuma shine maganar auren Mu'azzam!...... Kowa Afalon saida yad'ago ya kalli baffah, musamman ya khaleel da k'irjinsa yay tsawar hadarin gabas Na tsakkiyar ogusta Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review

Popular Books