Book
dan sarki complete
By Bintu Ahmad
   

About this book


Motocine sunkai guda goma shabiyu suna tafiya cikin kwanciyar hankali akan hanya kamar basuson motsawa wanda ke sauri baxai iya bin irin wanna tafiyar ba. Bakin wani katon gate naga sun tsaya, sai naga wani rubutu jikin gate din, sai da nakalla sosai naga an rubuta " *MASARAUTAR ZAZZAU*". Ina cikin kallon naga anbude gate din, motocin suka shiga daya bayan daya a tsanake banyan sunyi parking naga gaba daya kuyangi da barorin dake gurin sun zo sunyi tsaye cikin layi fadawan dake cikin motocin da bodyguards din suma suka fito suka tsaye amma nacikin mota banga kowaye ba.(a zuciya nace amma wannan yarinyar akwai jan aji) 30 mints latter Suna nan tsaye basu bar gurin ba kuma nacikin mota bai fito ba sai kawai gani nayi anbude motar akasalan ce, MASHA-ALLAH shine kawai abunda naji bakina ke iya furtawa a lokacin da idanuna suka yi tazalo da wani kyakkyawan hannu banyan kamar sec. 30 sai, ainihin mai hannun yafito(ashe) namijine kai wannan kasaita haka, fitowar shi yayi dai dai da lokacin da kuyangi., barori harmada fadawan ke gaidashi amma saboda kasaita kamar ma ba da shi suke ba nan ne fa aka fara kirari DAN SARKI jikan SARKI yarima me jiran gado badon angaji da SARKI ba sai don haka abun yake sai, alokacin yadaga musu hannu alamun su dai na saboda shi ya tsani yawan magana ko bashi keyiba. Kofar wani guri naga anbude mashi yashiga wani palour ne yashiga mai masifar kyau komai na palourn white ne tiles din gurin yana walkiya saboda samun gyara ga fararen bubs na haska gurin, kaitsaye ya wuce sai naga ya nufi wata kofa ya bide wannan karon da kanshi ya bude saboda sashen ma kamar ba kowa aciki wani corridor naga yabi sai yashiga wani palourn kuma wannan kam milk ne paint din sai kujeru red da touches din white acikine naga wata Mata mai Dan shekaru amma gayu da hutu sun boye shekarun kishingide take akan tumtum shima kalar gujerun gurin nega kayan marmari agaban ta tanaci cikin kwanciyar hankali, ya xo ya duka gabanta sai yan xu na ji muryar shi irin lion

Please login or create an account to leave a review