Book
fahimah 1
By Sumayya Abdulkadir
   

About this book


Ko yaya FAHIMAH zata yi da auren mijin da baya son ta? Bai kuma taba son ta ba a rayuwar sa? Don kawai ita ba kyakkyawa bace ba koko don asalin ta ne? Shin kyau shine kadai mizanin da za'a dora a so mace akan sa? Koko uslin ta ne yasa UWAIS dan asali yake gudunta? A wurin mahaifiyar sa Haj. Safeyyah-Basudaniyyah, mace ko da zubarjadu da yakutu aka kera ta to bazata auri kyakkyawan dan ta Uwais ba face FAHIMAr ta...... Fahimar da bata mallaki komai ba da zata jera kanta matsayin matar Uwais.... Fahimar data tsinto a *orphanage* duk da haka take son hada jini da ita fiye da kowacce mace a duniya... a wurin Haj. Safeeyah HALIN MUTUM SHINE YAKE SAWA A SO SHI amma ba asali ko zubin halitta ba.....shin soyayyar miji ko ta mahaifiyar sa wanne ke zaunar da mace din-din-din a gidan aure?? Shin matar so.... AMRAH, da matar matar shige wadda anka ce bata daraja....FAHIMAH, wacece zata yi nasarar sace zuciyar gwarzon miji irin UWAIS ABDULKARIM SHAGARI??? -Takori Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review