Book
gidanaurena
By Safiyyah Ummu-Abdoul
   

About this book


"Afaf wai me ke faruwa ne gidanku. Na rasa ganewa jiya da aka biyo dasu Aahil gidan nan Aaida ke ce min ita gidan nan zata dawo ku kullum se kunyi faďa, haba Afaf ina kika kai iliminki?" Haj chinyere ta faďi ranta alamun ba daďi. Shiru ya d'auki wajen, ganin hakan haj Chinyere ta cigaba da faɗin "kowa da kike gani yana cikin matsalar auratayya, iya taku da rashin datse communication tsakanin ma’aurata ke kawo kwanciyar hankali, faɗa min me ke faruwa? Kin san baki da uwar da ta fi ni ko? Kar ki fara min karya don ba zan dauka ba." Maimakon ta bada amsa, Kuka sosai Afaf ta saki wanda babu wanda ya kalleta balle yace mata kiyi shiru. Chan de ta fara cewa "Na tsaneshi Ummi, ko ganinsa bana son yi. Ummi ba Affan ďin da na sani ba ne, wannan mayunwacin zaki ne ba miji na Affan ba" faďin Afaf tana mai share hawayen ta da hannuwa biyu. Kallon ta surukarta ta tsaya yi chan dai ta miko mata wasu takardu sannan tace "Yanzu dai abinda nake so, rubuto min duk abubuwan da yake miki da bakya so" "Ummi takardun nan bazasu isa ba na faďa miki ya zama wani irin mayunwacin zaki. Ummi na tsane shi wallahi" Afaf ta faďi tana mai nuna alamun gajiya a zancen. KU BIYO MU CIKI DON JIN YANDA ZAA KAYA DA HANYOYIN GYARA MATSALARTA Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review

Popular Books