Book
hawayen zuciya 1
By Lubbatu Maitafsir
   

About this book


Tun asalin duniyar Nasreen Izzaddeen, ba ta san akwai wata soyayya, bayan ta Aqeel Mukaila ba. Tun bata san yana rayuwa a doron duniya ba take cin karo da shi a mafarkinta a duk lokacin da ta kulle idanuwanta. Zanen fuskarshi na daya daga cikin ababen da suke bata nishadi a kasan zuciya. Sai dai duk wannan abun, Aqeel Mukaila bai san da zaman kaunarta a gare shi ba. A bangare guda akwai Dakta Aqaq Saifullah mutumen da ya sadaukar da komai nashi dan ganin ya tsamo ta daga tashin hankalin da rashin lafiyarta ta jefa ta. Sai dai kuma soyayyar Aqeel Mukaila ta kulle idanuwan Nasreen wurin ganin kaunar da Dakta Aqaq Saifullah yake jifarta da shi. Kaddararta, larurarta, da tarin walagigin da rayuwa ta dinga yi da ruhinta ba su sa ta yi kasa a gwiyoyinta ba. Amma kuma ya labarin zai kasance a lokacin da wani shafi na gagarumar soyayya ya bude tsakanin mutumen da ta sadaukarwa komai na zuciyarta tare da yar uwar tagwaicinta? *** Salon labarin ya sha banban da na sauran labaran da kuka saba karantawa. zubin labarin, daban yake da duk wanda ya san zubin labarina. Akwai chakwakiya da yawa a cikin HAWAYEN ZUCIYA, sai dai na muku alkawarin ba za ku taba da na sanin sayen labarin ba. Na yi alkawarin warware muku duk wata tirka-tirka da na shirya a sannu. Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review

Popular Books