Book
kashe fitila complete
By Bintu Ahmad
   

About this book


Hankalin malamin Civic Education da kusan duka daliban yana kan monita wadda aka sanya rarraba takardun test da akayi satin da ya wuce. Wannan ya bawa 'yan mata biyu cikin daliban da suke zaune a layin farko daga tsakiya damar karasa shirin abin da suke kullawa tun safe. Daya daga cikinsu ce ta rike ciki tare da kwalla kara iya karfinta sannan ta sulale a kasa ta kwanta. Kafin malamin da sauran su ankara dayar ta durkusa a gabanta tana jijjigata a hankali da muryar kuka take cewa "Rumana me ya sameki, tashi don Allah, wayyo...." Murmushi ne yaso kwacewa Rumana ai kuwa taji kyakkyawan mintsini daga wurin Yusra kawarta "don ubanki idan kika tona mana asiri wallahi cewa zanyi ba dani akayi ba" Tsabar tsoro ne yasa Yusra yin zagin. A lokacin malamin har ya iso, sauran 'yan aji duk an zagaye su ana tambayar me ya faru. Yusra harda kukanta tace haka kawai ta ga Rumanan ta fadi. Health prefect aka kirawo daga ajinsu tare da taimakon Yusra da wata malama suka kai Rumana karamin asibitin cikin makarantar. Sannan aka nemi numbar makusancinta wanda ya kasance kawunta aka kira shi. Bayan an saka mata allura ana yi mata karin ruwa ne kowa ya fita sai likita da Yusra. Suna jin shiru Rumana ta bude idanu tare da saukowa daga kan gadon ta durkusa a gaban likitan "doctor ka taimakeni idan Uncle dina yazo ka fada masa ulcer ta kusa cinye hanjina" Duk da ya dauki maganar rainin wayo amma bai san lokacin da dariya ta subuce masa ba. Sai kuma yayi saurin daure fuska. "Nayi miki kama da abokin wasanki ne ko me?" Yusra ma durkusawar tayi "idan baka taimaketa ba wallahi yunwa zata kasheta a gidansu. Ulcer din gaske ce zata kamata" Juyawa yayi zai fita Rumana wadda ta tabbatar idan hakkansu bai cimma ruwa ba yau kila banda yunwa jikinta sai ya gayamata a gida bata san lokacin da ta fizge hannu daga jikin allurar ta ruga ta tare kofar ba "idan baka taimaka min ba wallahi zanyi muku hauka a asibitin nan. Ka fada masa mugun ciwo ya kamani a kaini gidanmu kada na mutu a nan" Saroro yayi yana kallonta. Bai ankara ba ya ga ta nufi gadon dakin ta daga shi da yake ba wani nauyi ne dashi ba ta kifar. Dan tebur din kusa da gadon ma hantsila shi tayi tana ihu da kuka. Yusra wadda tare sukayi shirin ciwon karyar ma sai da ta tsorata ganin da gaske Rumana tana neman yin hauka. Suna haka likitan yana kokarin riketa taji muryar kawunta daga dan karamin reception din yana tambayar inda take. Idanunta cike da hawaye ta sake kallon likitan alamun roko da neman agaji. Tausayi ta bashi, ita kuwa Yusra kuka take yi. Awaisu yana shigowa dakin ya ganta biji-biji kamar anyi wasan kura da ita. Ga hawaye ya wanke mata fuska. Da saurinsa ya karasa inda take ya rikota "Rumana me ya same ki? dena kukan ki fada min abin da kike so" Kasa magana tayi sai kukan da ta cigaba da yi. Ba a son ranta tayi wannan abin ba amma idan ba gaban iyayenta ta koma ba bata jin zata iya cigaba da hakurin zaman gidansa. Hankali a tashe ya dubi likitan "me ya sameta?" Hadiyar yawu yayi yana kallon yadda 'yan matan suka tsare shi da idanu "uhmm a binciken da nayi yarinyar nan tana fama da ulcer sosai har tana neman lahanta mata hanji" mamakin kansa yayi da biye musu harda aron kalamansu. Girgiza kai yake yi alamun rashin yarda "Ulcer, ulcer ciwon yunwa? Mtsew, ba dai a gidana ba wallahi." "Abin da bincike ya nuna kenan ranka ya dade" Tuni likita ya fara tsorata kada a daga maganar gaba. Harzuka yayi "kasan ko ni waye zaka kira min ciwon yunwa? To ko maigadin gidana bazai kira yunwa ba balle 'yata" Gaban likita ya fadi a zuciyarsa yace 'yarsa kuma, wace 'ya ce zata yiwa iyayenta sharri irin wannan. Harara ya jefa musu duk da ba kallonsa suke yi ba. Awaisu ya katse masa tunani " kaga ka sallameta zan kaita babban asibiti." Bai jira amsarsa ba ya ya durkusa ya dauko takalmanta ya saka mata sannan ya kamata suka fita. Wani irin tausayinsa ya kamata. Sai dai ko ana muzuru ana shaho da yardar Allah sai ta koma garinsu. Suna shiga mota taji ya umarci dreba da ya kaisu asibitin kudi da iyalan gidansa suke zuwa. To kada karyarta ta kare kawai sai ta sandare masa tana mimmikewa. Hankalinsa ya kara tashi. "Uncle babu inda zani, ka mayar dani gida na mutu gaban Mama. Kada na mutu ban sake ganinsu ba" A take ta karyar masa da zuciya. Asibitin dai yasa suka karasa sai dai a binciken gaskiya an tabbatar masa da gaske bata da kuzari. Tana bukatar hutu da abinci mai gina jiki. Wannan jawabi ya sanya shi cikin rudani. Duk yadda yaso su kwantar da ita fafur taki yarda ita Mama kawai take son gani. Gida suka koma yayi ta fadan yaya akayi bata cin abinci ba'a sanar dashi ba. Maamu mahaifiyarsa ita tayi jinyar Rumana a ranar. Da gaske ta rinka sambatu tana kiran babarta ko runtsawa basuyi ba. Dole washegari yayi shiri shi da dreba zai mayar da Rumana gida. Sai dai yana tunanin me zai fadawa dan uwansa a matsayin dalilin da yasa ya dawo da ita. Suna fita Maamu ta leko ta tagar dakinta tana kallonsu. Hawaye taji ya taho mata mai zafi tana tunanin yadda karamar yarinya ta samarwa kanta mafita. Ita kuma ta yaya zata ta bar gidan dan da ta haifa a cikinta?

Please login or create an account to leave a review