Book
kawaliya
By Maje El-Hajeej Hotoro
   

About this book


A wata Nahiya, a wata Kasa, a wani Yanki, a wata Jiha a wani Gari a Wata Kabila, wasu Mutane mabambanta ra’ayi da addini sun tattara waje guda ta hanyar haɗa ƙarfi da ƙarfe domin sauya salon tunanin al’ummar Duniya. Sun tara tarin tawagar masheƙa da ke iya sheƙe miliyoyin rayukan bil Adama ta hanyoyi da dama ba tare da shakka ba. Shagalallu ne kuma gafalallu ga aikata kowace irin aika-aika matuƙar Hakan zai gamsar da muradin zukatan su. Sun yi matsanancin nisan kiwo a baƙin kwazazzabon fito na fito da duk wani abu da ya kasance Halali ne. Sun kurmance dumu-dumu a cikin kwaɗayin kwaikwayon yanayi da sigogin rayuwar ƙazaman dabbobi ababen ƙyama. Sun makance ga tsananta adawa da Mahaliccin Sama da ƙasa ta kowacce hanya. Suna da gungun attajirai da matsafa a kusan kowane lungu da saƙo kamar yadda suka mallaki mahaukacin ƙarfin ikon tasirin faɗa a ji a wasu sassan ƙasashe masu gawurtaccen ƙarfin tattalin arziƙi. Babban fata da ƙudirin su shine yadda za su yi da’awar su ne Gumakan da za a riƙa a matsayin ababen biyayya da bauta sau da ƙafa. A tunanin su rayuwar Duniya ba komai ba ce face Kawaliyar da kowa zai sarrafa tunanin sa yadda ya so ba tare da biyayya ga kowane dokokin addini ko na kundin tsarin mulkin ƙasa ba. Yarda da su, zaman lafiya ya zama tarihi a gareka, kamar yadda bijire musu ka zama abin farautar su dare da rana. Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review