Book
kisan gilla 1
By Abdulaziz sani m gini
   

About this book


A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude anyi wani babban birni mai suna madinatul haswar a cikin daular larabawa birnin madinatul haswar ya bunkasa a kan karfin arziki girman kasa, karfin mayaka da yawan al umma sarkin dake mulkin birnin madinatul haswar ya kasance adali mai tausayi da jin kan talakawa ana kiransa da suna HISHAM IBN UBAIDA . SARKI HISHAM yana da matar aure guda daya jal mai suna shamilat wadda ta kasance yar wani babban sarki mai mulkin wata kasa da ake kira da hushush ana kiran wannan sarki da SAHIBUL HILAYAT sai da sarki hisham ya auri shamilat da shekaru goma sha daya sannan Allah ya albarkace su da samun juna biyu nan fa sarki hisham da shamilat suka cika da tsananin farin ciki domin a duniya basu da wani buri wanda yafi ganin sun sami haihuwa saboda a shekarun baya babu abin da basuyi ba, domin su sami haihuwar amma abu ya gagara, lokacin da mahaifin shamilat ya samu labarin cewa 'yarsa ta sami juna biyu sai ya kamu da tsananin farin ciki fiye da ita kanta shamilat din da mijinta saboda shi kuma bashi da burin da yafi yaga jikansa kafin ajali ya riske shi kasancewar tsufa ya riske shi a ko yaushe ta Allah zata iya kasancewa Al amin Ahmed Misau, Guyson nake magana, bisa wannan dalili ne sarki sahibul hilayat ya tashi manzanni da dukiya mai yawa ya aiko su izuwa ga sarki hisham yace ga wannan ayi renon ciki kuma idan haihuwa tazo daf yana son shamilat ta je gida ta haihu, yayin da wannan sako ya isa ga sarki hisham sai hankalinsa ya dugunzuma domin baya son ya rabu da matarsa dai dai da dakika daya amma kuma yana matukar jin nauyin surukin nasa don haka sai ya amince da hakan ita kuwa shamilat sai ta kamu da matukar farin ciki saboda a rayuwarta babu abinda take so sama da ta kasance tare da mahaifinta a ko yaushe saboda ita kadaice 'yarsa a duniya sarki Hisham yana da dan uwa yarima ZAMARU wanda ya kasance azzalumi kuma mara imani mai tsananin son duniya uwa daya uba daya suke dashi da hisham, a zahiri yarima zamaru yana nuna cewa yana matukar kaunar dan uwansa sarki hisham amma a karkashin zuciyarsa babu abinda ya tsana sama da shi ba wani bane ya haddasa wannan gaba ba a tsakaninsu face kawai hassada da kyashi da kuma tsananin son KARAGAR MULKI TUN mahaifin su sarki hisham na raye ya futa cewa hisham ne zai gaje shi daga wannan lokaci ne yarima zamaru yaji ya tsani dan uwansa sarki hisham ya fara tunanin hanyar da zaibi ya kawar dashi daga doron kasa sau bakwai yarima zamaru yana bayar da kwangilar a kashe hisham amma yana kubuta kasancewarsa sadauki mai dakawa maza gumba a hannu Guyson nake magana Al amin Kenan Lokacin da yarima zamaru yaga ya kasa ganin bayan sarki Hisham sai ya zuba ido izuwa lokacin da tsufa zasu riskeshi har rai yayi halinsa saboda ya tabbatar da cewa indai babu sarki hisham dole shine zai hau karagar mulki, ana cikin wannan hali ne na jiran lokaci kwatsam sai shamilat ta sami juna biyu hm Al amarin da ya kara dugunzuma hankalin yarima zamaru kenan saboda ya san cewa idan matar hisham ta haihu to fa sarautar ta kara yi masa nisa, a ranar da zamaru ya sami labarin cewa shamilat ta samu juna biyu sai ya kasa zaune ya kasa tsaye har dare ya raba bai rintsa ba Babban abinda ya kara jefa shi cikin bakin ciki shine shima matarsa ba ta taba haihuwa ba don haka duk ranar da ya mutu shi kenan bashi da magajin mulki, cikin tsakar dare yarima zamaru na kai kawo a cikin turakarsa ya kasa barci sai matarsa sarima ta farka daga barci koda taganshi a tsaye yana kai kawo saita dube shi cikin tsananin damuwa ta mike da sauri tasha gabansa tana mai rike kafadunsa, Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review