Book
magana jari ce 1
By Abubakar imam
   

About this book


Wannan littafi, Magana Jari Ce, 1, yana cikin littattafai guda uku da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta a cikin wata shida na zamansa a Zariya a shekarar 1936. Dalilin zabo shi kuwa ya rubuta wadannay littattafai shi ne ya shiga wata gasa to rubutun littafi a sheka rar 1933 ya kuma ci nasara da littafinsa na farko 'Ruwan Bagaja'. An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin Kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil to Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta 'Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen Raga labari mai ma'ana ya sa Dr. R. M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya roki a ba da shi ato daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya. Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rokon ya kara rubuta wasu littattafan. A can ya rubuta 'Karamin Sani kukumi' cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya roka a dawo da Imam Zariya a koya mashi aikin edita ya zama editan jaridar farko to Arewa. Shine ma ya rada mata suna `Gaskiya Ta Fi Kwabo' aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939. Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin 'Yakin Duniya Na Biyu' watau `Yakin Hitila' da ya ba suna 'Tafiya Mabudin Ilmi'. Wannan littafi ya ba da labarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Africa to Yamma zuwa Ingila a jirgin ruwa a shekara 1943. Wani mashahurin littafi kuma da ya rubuta shi ne 'Tarihin Annabi da na Halifofi' wanda aka fara buga shi a shekara 1957 lokacin nan yana shugaban Hukumar Daukar Ma'aikata to Nijeriya to Arewa. Alhaji Dr. Abubakar Imam shi aka fara nadawa Kwamishinan Jin Kararakin Jama'a a shekara 1974 a Jihar Kaduna, lokacin ana kiranta Arewa to Tsakiya. Ya rasu yana da shekara 70 a duniya ranar Juma'a 19 ga watan Yuni, 1981. Alhaji Abubakar Imam ya rika cewa wannan aiki da ya yi, na talifin 'Magana Jari Cc' ya yi masa amfani ainun. Ya kan cc wannan aiki shi ne ya ba shi damar zama tare da mashahurin Baturen nan na talifin Hausa, Dr. R. M. East, O.B.E. Ya cc daga gare shi. ne ya koyi duk dan abin da ya koya na game da talifi. Abin mamaki, shi kuma wannan Bature, Dr. East O.B.E., a wajen `Mukaddamar' da ya yi da Turanci tun farkon buga 'Magana Jari Ce', ga abin da ya ce : 'Muna godiya ga En'e to Katsina, saboda taimakonsu, da hangen nesa da suka yi, har suka yarda, suka ba mu aron Malam Abubakar Imam. Suka yarda, ya bar aikinsa, na koyad da Turanci a Midil to Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi wata shida domin ya taimake mu, mu sami wadannan littattafai a cikin harshensa. `lyakar abin da mu ma'aikatan wannan ofis muka yi, na game da talifin wadannan littattafai, shi ne aiki irin na ofis, na shirya al'amuran, yadda suka kai har aka buga su. Ban da wannan sai kuma taimakonsa da muka yi na tattara masa littattafai iri iri, don ko zai kwaikwayi wani samfur. Sai fa, kuma wajen shiryawa bayan da ya rubuta. 'Kai, in dai har muna da wani abin da za mu yi kirari mun yi, .game da talifin wadannan littattafai, to, babban abin kirarimmu kawai, shi ne yadda muka yi har muka binciko wannan malamin talifi'. 1982 N.N.P.C. Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review

Popular Books