Book
rayuwar rayhanah 3
By SUMAYYAH ABDULKADIR
   

About this book


Sauran kadan ta tsuge da zawo da ta hango Jawahir ta nufosu da sassarfarta. Da karfi ta ce, “Yaya Khalipha ka cika min hannu, ga Jawahir nan”. Lokaci guda kuma tana kici-kicin kwace hannun nata daya rike cikin nasa da karfi kamar zai balla ta. Amma Khalipha ko gezau bai yi ba, juyawa kawai ya yi yana tsimayen isowar Jawahir din. Mikewa ta yi da karfi ta fizge hannunta saura kadan ta fadi. Cikin zafin nama ta zauna a kan kututturen iccenta tana kokarin dai-daita numfashinta, nutsuwarta, bugun zuciya da yanayin fuskarta kafin isowar Jawahir. To ita ma Jawahir din duk da ta ga abin da ta ganin, amma da yake wayayya ce ba ta nuna komai a fuskarta ba, a zuciyarta cewa ta yi, “Na san wata rana irin wannan na zuwa, tsakanin Raiha da Yaya Khalipha, Intimacy din ya isa, haka kulawar da suke wa junansu a gida kadai abin a digawa ayar tambaya ne. Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review

Popular Books

YAKANAH 2

YAKANAH 2

47 reads
5