Book
silar ajali
By SAFIYYAH UMMU ABDOUL
   

About this book


Duk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani matashi dake kauyen da makwabtan kauyukan sun shaidata ne a matsayin daliba mai zuwa makarantar boko. Iyayenta basu da kudi, basu mallaki komai ba sai ita da kanwarta AMINA, daga su sai gatarin faskaren da mahafinta malam TANKO ya gada a wurin kawunsa, daga nan sai tukunyar da Rahanatu ta sani da ake dora musu abinci ba kullum ba. Kullum bata manta maganar babanta "karatun ki shine hanyar ceton mu, ke kamar gona ce da muke shuka muke fatan girban albarkacin noman mu anan gaba, karatun ki ne zai sa mu san dadin cire kudi mu biyawa kanmu bukata, karatun kine zai sa wata rana mu daina lissafa abincin da muke ci, karatun ki ne zaisa wata rana mu iya siyan sutura har mu manta adadin wadda muka mallaka, karatun kine zaisa a rika tunawa damu a matsayin masu rufin asiri. Dan haka kada kiyi wasa da karatun ki rahanatu" ba zata yi ba, saboda tana so taga iyayenta sun fita daga talauci. Ta sha alwashin haka. Sai dai a hanyar ta ta zuwa makarantar taci karo da shaidanin yaro HADI ALJAN. Yaron sarkin garin, yaci alwashin lalata rayuwarta koda ta hanyar fyade ne, bata bashi goyon baya ba, amma kuma ba zata iya hana shi ba Ba zata fadawa iyayenta ba saboda kada hankalinsu ya tashi Kota fada musu ba zasu iya komai ba babansa ne sarki. Ba zata kuma daina zuwa makaranta ba saboda canne fatansu yake. Ba zata iya salwantar da rayuwarta ta yarda dashi ba dan zai lalata rayuwarta. A haka ba yadda zata iya, yayi mata fyade. Ba zata iya fadawa iyayenta ba, duk da saida ta wuni a cikin gona cikin jinni, aka samu mai taimaka mata ta ceceta. Cikin da ya bayyana a jikin rahana shine ya zama silar tarwatsewar iyayenta da ita. Har ta tsinci kanta a birni.... A cikin tarragon rayuwa mai tsananin daci da burin daukar fansa... Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review

Popular Books