Book
siradin rayuwa 3
By SUMAYYAH ABDULQADIR
   

About this book


J irgin (American Airways) ya sauke su a birnin Ikko da karfe tara daidai na safe. Sai da kowa ya fita amma Al’ameen da Ihsan ba su ko motsa daga “seat” xinsu ba. Gaba xayansu jikkunan su sun yi sanyi, domin a take zazzafan zazzavi ya rufe Ihsan, ba su san da fuskokin da za su aro su dubi iyayensu ba. Sai da wata ma’aikaciyar jirgin ta yi masu magana cewa za a rufe jirgin, sannan ne Al’ameen ya tuna cewa shi fa namiji ne, ya rungume matarsa da hannunshi na dama a yayin da na hagun ke rike da ‘yar kyakkyawar jakarta ‘Japanese” a haka suka soma tako matattakalar jirgin cikin nutsuwa har suka taka kasarmu mai ximbin albarka. Dole idan ka kalle su sai ka maimaita su kuma yi bala’in ba ka sha’awa. Kwarjini da cikar zati irin na Al’ameen da ke sanye cikin expensive Italian suit, kalar baki da ratsin fari sol sun taimaka ainun wurin kara fiddo ilhama da cikar zatin shi, ya saya kwayar idon shi cikin bakin dark-spaces da ganinsa dai ka ga bakon Ba’amurke. To haka itama Ihsan xin tamkar aljana take don kyau, baby face gareta mai xauke da kayatattun idanu tare da kyakkyawan dogon karan hanci da gassun gira mai tsari. Yarinya ce ‘yar gajeriya mai jiki kuvul-kuvul, kamar na tarwaxa saboda tsabar hutu tamkar ba bakar fata ba, domin tun fil’azal ita brown ce, sai kuma zaman kasar sanyi da jin daxin samun gwarzon miji irin Al’ameen Bello, da suka kara wanke ta tas.

Please login or create an account to leave a review