Book
umm adiyya
By AZIZAH IDRIS M.
   

About this book


Babbar yatsar hannunsa na dama yake kaɗawa kan sitiyarin motar, yana tafe yana tunanin abubuwa da dama. Ƙwarai ya san cewa ba ƙaramin kuskure ya yi ba da ya sake barin Umm Aɗiyya ta shiga rayuwarsa. Koda kuwa ta fuskar aiki ne, duk da kasancewar ba yadda za ayi ya yakice ta daga rayuwarsa, saboda abin da ya haɗa su ba ƙaramin abu bane da zai warware a dare ɗaya, abin da ya haɗa su dangataka ce da ba ta rabewa ba, a tunaninsa ya mance da ita, ya sa ta a gefe, ba za ta taɓa tayar masa da abubuwan da ya zaci ya adanasu ya ɓoyesu a wani lungu a can cikin ƙirjinsa ba, sai dai yau abin da ya gani a tare da Adiyya, sun motsa masa abubuwa da dama masu daɗi da masu ɗaci. Amma ya zama dole ya dubi ɓangaren daya dace ya yi aiki da shi, saboda hakan zai fi fishe su, daga shi har ita. Har rana mai kamar ta yau ba zai taɓa mance abinda ya faru ba. Birki ya ja da ƙarfi, a dalilin wata motar da suka kusa yin karo, ashe tsabar tunani, ta sa ya bar kan hanyarsa ya hau wata daban. "Zaid Abdur-Rahman ka wuce haka!" Ya faɗa a bayyane, yayin da ya yanki kwanar (Darussalam Close da ke Wuse 2), inda shiryayyen gidansa yake. Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review