Book
zubar kwalla 1, 2 and 3
By AZIZAH IDRIS M.
   

About this book


Rahaanen Nana, Rahanen Terawa. Sunan da ake kiranta kenan tun da kuruciyarta sai dai Rahane bata san dadin kuruciya ba kaman ko wani yaro mai shekarunta, saboda yanda mai duka ya aiko mata da jarrabawar rasa mahaifinta a dai-dai wannan gaba. Rashin mahaifi ya janyo mata rashin mahaifa da nisantar mahaifiya inda ta fada rayuwar bauta a gidan yarta Adda Fatu. Ta zaba mata rayuwar kyara, ta hane ta jin dadinsa a lokacin da yaranta suke jin dadin nasu rayuwar ta zamo musu 'yar boyi. Rahaane tayi gamo da masoyi na kwarai wanda take fata zai dauketa daga wannan rayuwar, ga kuma Adda Fatu ta fitar mata da nata zabin sa'an mijinta. Imraan Abdl-Jawaad dan gata, dan kwalisa wanda baya neman abu ya rasa. Gani daya Allah ya hada zuciyarsa da Rahaanen Terawa. Bashi da buri duk duniya illa ya mallaketa a matsayin mata koda ya kama yayi abun da aka dade ana nusasshi yayi ya gagara. Dr. Nasir Salihu, likita mai cin ganiyarsa, dan ajin gabawanda ya rike zumunci da iyalansa sama da komai. Sai dai matsala daya d ake ci masa tuwo a kwarya iyanda mai dakinsa take halin ko oho da amanar dake hannunsu ta 'yar marainiyar 'yar wansa da ya rasu ya bari. Hanya daya ne na samun zaman lafiyarsa da matarsa shine ya kara aure. Kuma ya ga matar da ta dace. Shin Rahane zatayi sa'an kare soyayyarta ko kuwa za a ci galaba a kanta ta fada gidan Dr. Nasir Salihu? Shin ta san shirin Dr. Nasir akan aurenta don tayi raino? Shin Imraan zai bari Rahaane ta subuce masa? Noticed an error in this book? Send a mail to flag@okadabooks.com to report it

Please login or create an account to leave a review