Book
zumuntar zamani complete
By Bintu Ahmad
   

About this book


*1*. Kuka take rusawa mai tab'a zuciyar duk wani mai sauraronta ,babu kuma alaman tayi niyan tsagaitashi, dan abinda yake damunta, yake ci mata rai yayi zafin da a ganinta idan ba kukan tayi ba baza ta samu sassaucin damuwarta ba. Kawunta dake zaune bisa kujeran palourn ya zuba mata ido cikin k'unar zuciya da matsanancin b'acin rai, wannan Kuka da take yi ba k'aramin tab'a mishi zuciya yake yi ba. Ji yake inama da zai iya magance mata damuwarta da yayi ko da kuwa shi zai zame masa damuwa. Yanzu babbar matsalar shi bai wuci rashin sanar dashi takamemmen damuwarta ba. Cikin dak'ushewar murya wanda yake ji kamar Shima yasa kukan yace "Rumaisa, Kiyi wa Allah ki fad'a min damuwar ki, kukan ki yana d'agan hankali ,ki taimakeni ki fad'an damuwarki ko Zan samu kwanciyar hankali. " Volume na kukanta ta k'ara har tana shid'ewa ta kuma dad'a dukunkune kanta cikin katon hijabin da ke jikinta. Cikin k'arin b'acin rai kawunnata ya dunkule hanunshi ya naushi kujera "Bull shit,"yace cikin karaji, Rumaisa Kiyi magana mana. " D'ago kanta tayi da niyyar yi mishi magana wani kukan ya sake sarke ta tayi saurin mai da kanta. Tasowa yayi daga kujeran yazo ya durkusa a gabanta, cikin sassauta murya yace "Maisa, kasheni kike son yi ko? " Kai ta girgiza alamun A'a. "To, Kiyi magana, fad'a min damurki Maisan Kawu. " Ya k'arashe maganar da rarrashi. Cikin cin zuciya da sarkewar murya tace," Kawu, Bobbo zai kasheni ,bazan iya ba na gaji ,wahalar ta min yawa kasheni yake son yi, bazan iya ba, bazan iya ba, na gaji Kawu, na....... " Tana fad'a tana jujjuya kanta. Numfashinta ne taji kamar zai d'auke ta yanke maganar taci gaba da shessheka. "Me KABIRUn yake miki, Maisa, fad'a min me ya ke miki. "cikin tashin hankali da tafasar zuciya yake magana idanunshi sun rine da b'acin rai. Ci gaba yayi da cewa "Maisa fad'amin abinda ya ke miki Wlh zan kashe aurennan, dole zan karb'a miki takardarki. " Maganarshi ta k'arshe tayi dadai da shigowar Kabeer, palourn idonshi a kansu. Wani irin bugawa zuciyar Kabeer takeyi kamar ta fito, Kallon tsana ya bisu dashi dukansu biyu kafin ya yi hanyar d'akinshi. "Kabiru! Kabiru!! kabiru!!! Duk Wannan kira da yake jera mishi cikin b'acin rai da zafin zuciya baisa ya juyo ba shigewa d'akinshi yayi ya rufo k'ofa. Bishi ya farayi Rumaisa tayi saurin tare shi "Kawu ka kyale shi zuciyarshi ba kyau kar Kuyi b'atacciya dashi. " "Zuciya? Waye bashi da shi, muyi abinda yafi b'atacciya ma in yaga dama, ba fa Zan kyale shi ba, Wlh akanki Zan iya aikata komai Maisa. " Ya na gama fad'ar haka ya tasamma d'akin Kabeer. Kwankwasawa ya shigayi yana kiranshi, idan ya amsa dutse ma ya amsa. K'arshe ya shiga jijjiga kofar har ya gaji dan kanshi ya koma ya zauna yana huci yana surutai "Zaka fito ka sameni anan dan ubanka, ni ba sa'anka bane, badai kace kai d'an iska ba, Zan gwada maka kalar tawa iskancin. " ita dai Rumaisa ganin abin yana neman yafi karfinta ta shige d'akinta ta takure gu d'aya. Saida Kabeer ya gama duk abinda zaiyi tukun ya fito, ga mamakinshi sai yaga Kawu bai tafi ba yana zaune. D'auke kanshi ya yi ya wuce zai fita, cikin zafin nama Kawu ya sha gabanshi ya rike kwalar rigar shi. Kallo Kallo suka shiga yiwa juna cikin tsantsan tsanar juna. kawu ne ya fara magana "Wato ga d'an iska ko, ina maka magana, Kayi wucewar ka, yanzu kuma kazo ka d'auke kai kamar bakasan da mutum a nan ba, wai kabiru me kakeji dashi ne? Ko Ubanka bai tab'a min rashin mutunci haka ba balle kai. " Sai a snn Kabeer yayi magana "Shi dama mai mutunci ne, rashin mutunci kuma a wurinka na d'auko." Fizge jikinshi yayi da karfi daga rikon da Kawu ya mishi yana cewa "Mind u, kada Ka sake yi min irin wnn abin, ko baka ga wanka nayi yanzu ba kake son b'ata min jiki da datti. " Yana gama fad'an haka yayi waje da sassarfa ya bar kawu nan tsaye yana huci. Motarshi ya shiga ya bata wuta. Shiko kawu Kwafa yayi yace "Sai na raba aurennan dan Ubanka daga nan yasa kai Shima ya fita... *Toh

Please login or create an account to leave a review