Adventure

The Trials of Maclean Agu

the trials of maclean agu

0 read
0
₦500.00

Maclean Agu is a budding banker with the hopes of a bright future until a failed robbery takes place in his bank and his fortunes spiral out of control. Does he have what it takes to regain the wheels?...

Available to read on app and web
BAKAR GUGUWA 1

bakar guguwa 1

0 read
0
₦200.00

Ya sake jifansa da wani irin mashi na aikin sihiri ja jawur dashi kamar karfen da aka curoshi daga wutar makera, Buniyatu ta tura wata 1ska ma1 tsananin karfi ta ture mashin ya tafi ya fada cikin wata korama dake gudanawa a tsakiyar lambun, ruwan cikin koramar ya kama tafasa saboda masifa nan take launin ruwan ya sauya ya koma ja jawur kamar jini. Matsafi Bahalu ya sake fusata da fushi mai tsanani ya yi karaji da kururuwa mai matukar karfi, ya daki kasa da sandar tsafin dake hannunsa, iska da bakar guguwa suka turnuke suka rufe wajen har sai da su Zuhairu suka daina ganin junansu, ya biyo ta cikin duhun bakar guguwar da nufin halaka Zuhairu, Buniyatu ta tura wani farin haske cikin bakar guguwar sai ga matsafi Bahalu ya bayyana tana ganinshi, ya daga sandarsa ta tsafi dake hannunsa zai makawa Zuhairu Buniyatu ta sanya hannunta ta ade Sandar bai same shi ba. Bahalu ya sake fusata ya kai mata sura cikin sa'a ya fizge kurtun sihirin da yake hannunta, wanda a tare da shi ne duk wani abu da ta gada na daga alkaluman sihiri yake ciki, Buniyatu ta yi karaji da kururuwwa ma tsananin karfi, saboda subucewar kurtun sihirin daga hannunta zuwa hannun matsafi Bahalu....

Available to read on app and web
BAKAR GUGUWA 2

bakar guguwa 2

0 read
0
₦200.00

"Ke dai kina cikin dimuwa da bata wadda ba za ta dawo da ke kan turbar gaskiya ba, kuma tun da kin yi zabi da kasancewa cikin wannan hali tare da jama'ar da ki ke tare da su, to ku yi Saurare da zuwan musibar da za ta riskeku ta kai ku ga halaka, ita ce za ta zama hanyar salwantar rayuwarku ba za ku taba kubuta daga gareta ku ketare wannan kogi da ku ke ciki ba," Yana gama ambaton wannan magana ya sake bushewa da dariya irin ta mugunta da zalunci sannan ya bace cikin bakar guguwar da ya bayyana a cikinta ya bar wajen, daga nan sai suka sake jin wata tsawa da rugugi mai ban firgici ya gauraye wajen can daga gabansu sai suka hangi ruwan kogin nan ya dare gida biyu ya yi tsiri sama, tsayinsa zai iya shan kan jirgin ruwan da suke ciki ya nutse da su su halaka, sannan sai wata iska mai karfi ta soma tura jirgin ruwan yana tunkarar inda ruwan kogin nan ya dare gida biyu za ta dulmiyar dasu su halaka, su Zuhairu suka ci gaba da addu'a don neman kiyayewar Ubangiji ya kubutar da su daga wannan musiba da suke ciki. Jirgin ruwan ya ci gaba da tafiya yana kara tunkarar inda ruwan kogin ya dare gida biyu zai dulmiyar da su su halaka....

Available to read on app and web
Air bender

air bender

0 read
0
₦100.00

Air bender series...

Available to read on app and web
When love sprints (part 1)

when love sprints (part 1)

20 reads
4.75
Free

Set in the 17th-century A.D, Oke, a young farmer, takes a huge risk to win the heart of the woman he loves. However, he soon discovers that his problems are far from over. He is plunged into dangerous situations that endanger his life and that of his heartthrob, Nkoli. Will their love survive the pressure to call it quits? The author uses an epic plot and a poetic voice to tell a story of passion, adventure, love, and courage at a time long before now....

Available to read on app and web
TAKOBIN ƊAUKAKA 1

takobin ɗaukaka 1

0 read
0
₦100.00

Lokacin da sarauniya lasmirat ta isa gidan boka Dayyubul-Barmas ta kaɗaita dashi a cikin turakar sa Nan take ta kwashe labarin abinda ta gani a cikin halarar tsafin ta ta zayyanewa boka Dayyubul-Barmas tun daga farko har ƙarshe, sannan ta ɗora da cewa Yakai wannan boka mafi girma a halarar tsafi kayi sani cewa Babban burina shi ne na auri mijin da yafi kowa Arziki a duniya sannan ina da burin na rayuwa kamar shekaru dubu biyu domin nazamo nafi dukkanin sarakunan duniya daɗewa a bisa karagar mulki, Yayin da boka Dayyubul-Barmas yaji irin buƙatar dake tafe da sarauniya lasmirat sai ya jinjina al'amarin a cikin ran sa, Tsawon daƙika arba'in bai ce uffan ba sai daga bisani ne ya dubi lasmirat yayi gyaran murya yace" ya sarauniyar kyawawan duniya kiyi sani cewa hakika kin zomini da al'amari mai girman gaske Hakika bakaramar hikima kikayi ba da kika bayyana bukatar a gareni domin shi ilimin tsafi kogi ne komai nutson ka a cikin sa baza ka kwashe Abinda ke ciki ba, Kuma kinsan masu iya magana na cewa Abin da Babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai hango ba, abin da bincike ya tabbatar mini ga me da bayanin ki shi ne. Matsawar kina son ki fi kowa ne sarki daɗewa abisa karagar mulki kuma ki auri mijin da yafi kowanne kuɗi a duniya to yazama wajibi ki mallaki abubuwa guda uku domin ki samu nasarar samun ruwan koramar matsafi Daryalu Da farko za,a nemo ruwan kogin ma'ul-hayatu, Sannan waɗansu zobunan tsafi dake ajiye a kogon fatalwa a can yankin kasashen Larabawa a wani daji da ake yiwa laƙabi da Husumul-kadar Abu na karshe shi ne kubar miftahul-daryal, Shi dai wancan ruwa zamu yi amfani dashi ne a lokacin da zamu shiga wani daji kafin mu isa inda koramar boka Daryalu takr, ruwan zai bamu kariya ne daga waɗansu musifu dake dajin, Su kuwa waɗancan zobuna zamuyi amfani da su ne a lokacin da zamu shiga gidan boka Daryalu rukuni na farko wajen sanya su a hannayen mu, Domin babu yadda za,ayi mutum ya shiga gidan face ya na ɗauke da waɗannan zobunan sihirin, Kubar miftahul-daryal kuwa zamu yi amfani da ita ne wajen buɗe gidan boka Daryalu Dazarar mun samu nasarar ɗebo ruwan koramar kinsha to shi kenan bazaki auri wanda yafi kowa talauci a duniya ba, Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo dai dai nan azancen sa sai hankalin sarauniyar lasmirat ya ɗugunzuma ainun Ta dube sa cikin alamun tsantsar damuwa tace" ya Sarkin bokaye shin taya ya zan mallaki waɗannan abubuwa kafin ajali ya riskeni Koda jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa Sannan daga bisani kuma ya fashe da kuka. Al'amarin da yayi Matukar bawa sarauniyar lasmirat mamaki kenan kuma ya ɗaure mata kai ta dube sa ta ce" ya uban bokaye shin ina dalilin wannan dariya,da kuka naka? Da jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya share hawayen dake sannan ya buɗi baki yace ya shugaba ta abinda ya sanya dariya shi ne bincike ya tabbatar mini dacewa a wannan zamani nine bokan da zan samu ɗaukaka fiye da kowa ne matsafi domin ya cika burin mahaifin mu. Abinda Ya sa ni kuka kuwa shi wani bakon jarumi zai rushe wannan ɗaukaka tawa ta yadda ko tarihina bata sake tunawa a duniya ba Kuma wannan jarumi ba wani bane face namiji da zaki aura har ki samu Haihuwa wanda yafi kowa talauci a duniya Sai dai iyakar bincike ne na kasa gano ainahin a nahiyar da saurayin yake, Domin jarumin yana yana ɗauke da waɗansu sirrika masu basa kariya, Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo dai -dai nan a jawabin sa, sai hawaye suka sake zubo masa, Nan take Sarauniya lasmirat taji ta kamu da matukar tausayin sa Dayyubul-Barmas ya cigaba da cewa ya sarauniyar kyawawa kiyi sani cewa bazaki taɓa fin kowane sarki daɗewa abisa karagar mulki ba face kin mallaki wata takobin da ake yi wa laƙabi da TAKOBIN ƊAUKAKA, A salin TAKOBIN ƊAUKAKA ta wani gagurtaccen mayaki ne ma'abocin addanin musulunc, Bayan shuɗewar jarumi Hilal ne wani mashahurin matsafin aljani ya sace takobin ya shiga halarar tsafi ta tsawon shekaru arba'in yana sana'anta takobin da sirrikan tsafi An kira takobin da suna TAKOBIN ƊAUKAKA ne saboda duk jarumin da ya mallake ta zai samu ɗaukaka a duniya Lokacin da aljani Sautul-Hidar ya kammala halwar sa sai yaga wani Al amari da ya firgita sa kuma ya ɗimauta sa, Abinda ya gani shi ne bazai taɓa samun amfani da TAKOBIN ƊAUKAKA ba ajali zai riske sa, Wani jarumi wanda bai kasance kowan kowa ba shi ne zai mallaki takobin ya lalata sirrikan tsafin dake jikin ta kuma ya ɗaukaka a duniya, Lokacin da aljani Sautul-Hidar ya ga wannan al'amari sai ya cika da baƙin ciki Kawai sai aljani Sautul-Hidar ya ɗauki TAKOBIN ƊAUKAKA ya caka a kirjinsa a saitin ƙahon zuyar sa, Faruwar hakan ke da wuya sai numfashin sa ya ɗauke komai na jikin sa ya daina motsi ya sandare,take gangar jikin sa ta zagwanye ta zama wani irin ɓakin ruwa mai yauƙi, Daga bisani sai ruwan ya rikiɗa izuwa waɗansu irin gabza - gabzan samudawan aljanu dukkanin suna shirye cikin wata irin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini da ban tsoro a hannayen sa rike da waɗansu irin makaman yaƙi masu barazana ga duk wata halitta mai numfashi, Koda bayyanar aljanun sai wani daga cikin su wanda da alama shi ne shugaban su ya ɗauki TAKOBIN ƊAUKAKA ya sanya ta acikin wata akwatu ta farin gilashi ya ɗauki akwatin da takobin ke ciki ya shiga sanya ta acikin waɗansu akwatin har guda dubu, Sannan ka sa dakarun aljanun izuwa kowace kusurwa ta gidan domin tabbatar da cikekken tsaro ga takobin...

Available to read on app and web
TAKOBIN ƊAUKAKA 2

takobin ɗaukaka 2

0 read
0
₦100.00

Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin shu'umar aljana da su sarauniya lasmirat, Sai lasmirat da yaslir suka wanzu suna kaiwa aljanar sara da suka cikin tsananin zafin nama JURIYA DA BAJINTA Duk sa'adda makaman su suka sauka a jikin aljanar sai kaji sun bada kara ƙal ƙal !! Tamakar karfe suka sara In banda lasmirat da yaslir suna cikin kariyar tsafi da tuni sun hallaka, Idan aljanar ta kaiwa yaslir da lasmirat hari da hannayen ta, idan suka goce duk abin da hannun ta ya sauka akai sai dai kaga ya tarwatse,idan kuwa a ƙasa ne sai ya haddasa wani rami zurfin gaske, Take dakaru da dawakan su zasu afka cikin sa suna ihu da kururuwar neman taimako, Nan fa waje ya cika da ihun mazaje mata da yara da matasa, Karafniyar ƙarafa ta cika dodon kunne, JINI DA KASA suka cakuɗu, ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, Lokacin da aka shafe dakika ɗari biyu da sittin ana wannan bakin gumurzu, Sai ya zama na cewa aljanar ta samu nasarar hallaka dakaru Fiye da dubu shida, Amma bata samu nasarar koda lakutar jikin su lasmirat ba sai ta cika da matukar mamaki kuma ta fusata ainun, Abin da ya bata mamaki shi ne ya akayi sarauniya lasmirat da saurayi yaslir suka kasance masu tsananin zafin nama, tabbas yau ta haɗu da takadiran jarumai, hakika rashin wannan nasara ƙasanta darajar ta ne da kimar ta, Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai ta canza salon faɗan ta yazamana cewa tana haɗa kai bugu da naushin hannu da ƙafa, Ai kuwa nan take labari yasha Bambam, domin a halin yanzu daƙyar su yaslir ke iya mayar da martani Idan ta daki gini ya tarwatse sai kaga duwatsun sun yiwa su lasmirat lugudan duka, Sai da aka shafe tsawon dakika dari da ɗoriya ana wannan fafatawa, Ana cikin wannan yaƙi ne aljanar ta kaiwa sarauniya lasmirat da yaslir wawan naushi da nufin yi musu farat ɗaya, Amma kafin hannun ta yakai gare su sai suka daka tsalle a sama tamkar an harbosu daga cikin baka suka bar kan dawakan su Sai gashi hannun ya sauka akan dawakan sun tarwatse tamakar an talitse tumatir, A daidai wannan lokaci ne yaslir da lasmirat suka sauka akan aljanar bisa tsakiyar kanta su shiga kafta mata sara babu sassauci, Nan fa yazamana sun riki ta aljanar yazamana cewa ta daina kaiwa dakaru hari Sai dai ƙoƙarin taga ta jefo su yaslir daga kan ta, ana cikin wannan hali ne aljanar ta samu nasarar damƙo su yaslir ta hannun ta ta matse su nan take suka sume sakamakon maƙurewar, Ashe ta samu nasarar karya ɗan yatsan yaslir, lasmirat kuma ta samu gocewar ƙashi, a hannun ta, Koda samun wannan gagarumar nasara sai aljanar ta bushe da shu'umar dariya Sai da tayi dariyar ta ishe ta sannan ta tsuke bakin ta kawai sai ta juya ta nufi kofar fita daga birnin tana mai koɗa kanta gami da yiwa kanta kirari, tana mai cewa " Saini GAWURTACCIYA uwar hatsabibai, GUGUWAR YAƘI nake mai share MAYAKA, ANNOBA ƊARI nake duk wanda ya Kusan ceni zai baƙun ci barzahu, Ni ne gararriya uwar gagararru, Haka ta cigaba da yiwa kanta kirarin tana lafiya a cikin birnin, Duk sa'adda ta ajiye kafarta ɗaya sai dai kaga ƙasa tana girgiza tamkar zata tsage abin da ke saman ta ya faɗa cikin ta Koda sauran dakarun suka ga abin da yafaru sai suka dunga ɗame kwari da bakan su suna Harbin aljanar Duk tsananin yawan kibban sai yazamana a banza domin ko gezau batayi ba Sai dai ma kaga ta sanya hannun ta ɗaya tana karkaɗe kibiyoyin kamar tana kaɗe ganyayyakin bishiya, Kwatsam bazato babu tsammani sai aka ji aljanar ta kurma wawan ihu kuma ta faɗi ƙasa tim, Ta saki su sarauniya lasmirat suka faɗo ƙasa babu alamun rai a tare dasu , Kuma akaga aljanar ta ɗaga hannayen ta sama tana mai roƙon gafara, ...

Available to read on app and web
TAKOBIN ƊAUKAKA 3

takobin ɗaukaka 3

0 read
0
₦100.00

Ranar da tafiya dajin Husumul-kadar tazo, sarauniya lasmirat, yaslir da Sunaila suka yi gagarumin shiri, Suka hau bisa dawakai suka nufi hanyar da zata sadasu da gidan boka Dayyubul-Barmas, Bayan lasmirat ta bayar da rikon sarautar ta a hannun waziri ukashat, Kuma waziri ukashat ɗin da sauran al'ummar gari sun yi musu rakiya har zuwa kofar gari, Lokacin da sarauniya lasmirat suka iso gidan boka Dayyubul-Barmas sai suka ja linzamin dawakan su suka yi turjiya, Su kayi cirko- cirko suna masu ƙarewa gidan kallo, shi dai gidan boka Dayyubul-Barmas yakasance ɗan madaidaici da aka ginasa da zallar duwatsun wuta masu ƙyalli, yana da kofa guda ɗaya da akayi ta da zallar karfen jauhari, Bakomai yasanaya su sarauniya lasmirat suka yi wannan cirko-cirko ba sai bisa ganin Kofar gidan a garƙame, kuma ya na lulluɓe da wata yanar gizo gizo Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai akaga boka Dayyubul-Barmas ya bayyana tsulum! a gaban su fuskar sa cike da annuri, Yana sanye cikin kyawawan tufafi na alfarma,sun yi matukar yi masa kyawu, a hannun sa yana rike da wata isgar tsafi,wacce take canza launi Lokaci zuwa lokaci, wani lokacin ta koma baƙa,shuɗiya ko Koriya, Lasmirat ta yi murmushi ga boka Dayyubul-Barmas daya ƙarawa fuskar ta annuri tace"ya abin dogaro na shin ina dalilin rashin bayyanar ka akan lokaci domin gudanar da wannan tafiya tamu? Dayyubul-Barmas yayi murmushi yace" ya sarauniyar kiyi sani cewa bakomai bane ya sanya ban bayyana akan lokaci ba sai domin na kara gudanar da bincike ne game da tafiyar tamu, Koda jin wannan batu sai lasmirat tace " ka gafarceni ya uban bokaye, Dayyubul-Barmas ya tari numfashin ta yace "ba sai kin wahalar da kanki wajen sanar da ni sunayen a bokan tafiyar ki ba, Yaslir da Sunaila, dukkan su ilimin tsafi ya bayyana mini abin da ya gudana tsakaninsu da su, Tabbas kin yi tunani mai kyau, domin Sunaila da yaslir zasu yi matukar taimaka wajen wannan tafiya tamu, Yanzu ina ganin abinda ya kamata mu fara yi shine tafiya domin ɗebo ruwan koramar boka Daryalu, domin hakan shi ne zai bamu damar fuskantar dajin Husumul-kadar, Koda gama faɗin hakan sai boka Dayyubul-Barmas ya kwallawa aljanin sa kira sau uku, Aljanin ya bayyana gaban sa ya kwashi gaisuwa, duk da kasancewar su lasmirat suna da dakakkiyar zuciya sai da suka razana da ganin aljanin, Aljanin yakasance garjejen kato karfaffan gaske,yana da rafkeken kai tamkar dutse,mai ɗauke da waɗansu manyan idanu jajaye,tamakar kwallon goriba,yana da katon hanci da rafkeken baki, sannan ya da manyan fuka-fukai guda shuda, Boka Dayyubul-Barmas ya dubi aljanin cikin nutsuwa yace"yakai Huzmal ibn kuddar kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka ɗauke mu izuwa Husumul-kadar domin ɗauko zobunan sihiri a cikin kogon fatalwa, Daga nan kuma mu huce izuwa inda ma'ul-diya'u yake mu ɗauko kubar miftahul-daryal, Yakai Huzmal ibn kuddar kayi sani cewa wannan shine aikin ka na ƙarshe da zaka samu ya ci Yayin da aljani Huzmal yaji wannan batu sai ya risina ya ce" An gama ya shugabana Yana gama faɗin hakan sai ya shimfiɗe gadon bayan sa boka Dayyubul-Barmas, lasmirat, yaslir da Sunaila suka hau suka zauna Sannan ya yunkura ya ya tashi sama ya na mai buɗe fuka-fukan sa yana mai keta gajimare, cikin sa wani irin azababban gudu na keta sa'a ...

Available to read on app and web
TAKOBIN ƊAUKAKA 4

takobin ɗaukaka 4

0 read
0
₦100.00

Mutumin mai siffa biyu ya bushe da dariyar mugunta bisa ganin wannan gagarumar nasara da ya samu akan su boka Dayyubul-Barmas, Dariyar tasa ta haddasa girgizawar kogon, a lokaci guda kuma ya tsuke bakin sa tamkar an aiko masa da SAƘON MUTUWA kawai sai ya nufi wata kofa a cikin kogon dutsen, Kwatsam bazato babu tsammani sai mutumin yaji an dankara masa wawan sara a gadon bayan sa, Saboda karfin saran sai da sai da takobin ta nutse a gadon bayan sa, Kawai sai ya kwarara ihu tare da waigawa bayan sa domin ya ga wanda ya sareshin. Ai kuwa yana waigwa sai yayi arba da jarumi yaslir hannun sa riƙe da zaratan takubba masu kaifi da tsinin tsiya, A dai dai lokacin ne jini yafara kwaranyo wa daga inda yaslir ya sare shi , Mutumin ya dakawa yaslir tsawa wanda ta sanya kogon ya amsa da karfi, Bisa mamaki sai mutumin yaga ko gezau yaslir bai yi ba, al'amarin da yayi matukar bashi mamaki kenan, Domin bai taba dakawa wata halitta tsawa ba face ta ɗimauce,ko ma ta rasa rayuwar ta, Wani tunani da ya faɗo masa shi ne, taya ya wani makami yayi tasiri akan sa Bayan cewa hakan bai taɓa faruwa ba, Lallai bakaramin kuskure kayi ba da ka manta da wannan bil,adama, Sa'adda halittar yazo nan a tunanin sa sai zuciyar sa ta kama tafarfasa tamkar zata kone jikin sa yakama kyarma yana tsuma tamkar mazari, Kawai sai ya miƙa hannun sa ya ɗauko wannan Gatari nasa Sannan ya kwarara wawan ihu ya ruga izuwa kan yaslir yana mai ɗauke da su boka Dayyubul-Barmas a ɗaure a jelar sa, Sa,adda yaslir yaga halittar ya rugo izuwa gare sa cikin mugun tanadi, Sai kawai ya gyara tsayuwar sa, lokacin da ya rage sauran taku Sai yaslir ya dako wawan tsalle tamkar an harbo sa daga cikin baka yana saman ya kaiwa halittar sara da takubban sa biyu a kafaɗa, Bisa sa,a sai gashi ya same Shi har jini na zuba a kafadar tasa Cikin gwanin ta yaslir ya yi katantanwa a sama sau uku ya dira ƙasa a bisa duga-dugan sa cikin gwanintar yaki, Sannan suka kacame da azababban artabu mai matukar muni,ban tsoro daban al'ajabi, Sai da aka shafe tsawon sa,a biyu ana wannan gumurzu babu sassauci, Tsawon wannan lokaci babu wanda ya samu nasarar lakutar jikin abokin gwamin sa, Duk sa'adda mutumin mai siffa biyu yakaiwa yaslir sara inda ya goce duk abinda gatarin ta sauka a kansa sai kaga wajen yayi rami mai zurfi, Idan akan Dutse ne sai Dutsen yayi bindiga ya tarwatse, Kafin cikar dakin talatin yaslir yafara galabaita saboda yadda yake zillewa harin mutumin, A dai dai lokacin ne kafafatun yaslir suka faɗa cikin wani rami a kogon kuma wani dutse ya danne sa, Wohoho! Wuya mai sa dole, shi kuwa tsoro na iya sawa mutum ya aikata abin da ko a mafarki bai taba tunanin zai iya ba idan yaga bala'o'i, Koda yaslir yaga halin da yake ciki kuma ya tabbatar da cewa idan har bai yi wani abu ba zai iya rasa rayuwar sa Sai kwai akaga yaslir ya sanya hannayen sa biyu ya ture Dutsen daya danne sa ta ƙarfin tsiya,kuma ya naushe sa da hannayen sa biyun cikin baƙin zafin nama take dutsen yayi sama tamkar an janye da ƙungiya ya daki fuskar mutumin mai siffa biyu, Take halittar ya ɗimauce ya gigice yayi jifa da gatarin sa ya sanya hannayen sa biyu akan fuskar sa yana rusa ihu,...

Available to read on app and web
FATAUCIN BAYI LITTAFI NA 1

fataucin bayi littafi na 1

0 read
0
₦100.00

Dakarun na cikin rarraba musu gurasar ne wani badakare ya miƙawa wata yarinya gurasar, Kafin hannun badakaren yakai inda na yarinyar yake, yarinyar tayi shammace sa ta ciri wata yar siriyar wuka a jikin sa ta caka masa a marainan sa, sannan ta sanya kafafun ta biyu tayi daki kafafun badakaren ya wuntsila izuwa Cikin tekun yana mai tsandara ihu, Al'amarin da ya janyo hankalin sauran dakarun kenan, suka zubar da abincin dake hannun sa suka zare makaman su suka ruga izuwa inda yarinyar take, koda ganin hakan sai yarinyar ta ɗauko wata doguwar igiya cikin wani irin zafin nama ta yiwa igiyar wasu ƙulluna,ta jefawa dakarun, Sannan ta daka wawan tsalle ta faɗa izuwa cikin Tekun tana rike da sauran igiyar a hannun ta, take igiyar ta zarge kafafun dakarun ta jasu izuwa cikin tekun. Koda ganin hakan sai sharkar Ya dakawa sauran dakarun tsawa dasu sake ɗaure fursunonin, kuma aka umarci masu tukin jirgin su tsayar da tafiya, sannan dakaru mutum hamsin inkiya dasu biyo bayan sa, suka ruga izuwa bakin jirgin, Ai kuwa koda tsayuwar su sai suka yi arba da gawarwakin dakarun da suka faɗo sun taso izuwa saman ruwan,gaba daya an yi musu yankan rago, Al'amarin da yayi matukar ba su mamaki kenan kuma ya harzuƙasu, Abin da ya basu mamaki shine yaza,ayi ace yarinya karama ta samu karfin yiwa zaratan dakaru sha biyar yankan rago, Cikin fushi sharkar ya umarci dakaru goma waɗanda suka kware wajen iya ninƙaya a ruwa, suka faɗa izuwa cikin Tekun,domin laluben inda yarinyar ta shiga, Kaico! Hakika rashin sani yafi dare duhu, domin da a ce waɗannan dabaru sun san abin da zai biyo baya da basu gangancin faɗawa tekun ba, Domin Abin da basu sani ba shi ne lokacin da suka faɗa Cikin Tekun wani katon kifi ya wangame bakin sa, yana hamma ai kuwa bisa sa,a sai suka faɗa a bakin sa kawai sai ya lamushe su yayi loma ɗaya dasu sannan yayi nutso izuwa cikin tekun, Nan fa yazamana cewa sharkar ya tura Gaba ɗaya dakarun dake bayan sa izuwa cikin tekun,amma ɗayan su bai taso a raye ba. Kwatsam Sai akaga gawarwakin dakarun birjik sun taso daga kasan tekun, Al'amarin daya kara firgita shugaba Yasiran da sharkar kenan...

Available to read on app and web
FATAUCIN BAYI 2

fataucin bayi 2

0 read
0
₦100.00

Koda samun wannan nasara dakarun suka shiga daure da gaba ɗaya fursunonin dake cikin jirgin ruwan, waɗansu irin murtuka-murtukan sarƙoƙi, Koda kammala hakan sai waɗansu dakaru na musamman suka shiga tuƙa jirgin aka cigaba da tafiya, sauran jiragen dakarun guda ashirin suka mara musu baya, Tafiyar sa'a uku kacal tawagar dakarun suka yi suka iso izuwa gaɓar tekun, Take dakarun suka fito da su Nabihat daga jirgin ruwan. Nesa kaɗan da inda aka sauka wani kasaitaccen birni mai dogayen gine gine, Kallo ɗaya zaka yiwa birnin ka fahimci cewa an kashe dukiya mai tarin yawa wajen gina sa. Batare da wani bata lokaci ba aka tusa ƙeyar su jaruma Nabihat izuwa birnin, Da yake a wannan lokaci su Nabihat suna cikin halin suma ne sai aka ɗora su abisa kan wani keken doki, Nan fa tsananin wahala ya sanya sauran jama'ar su Nabihat suka dunga yanke jiki suna faɗuwa kasa, sakamakon tsananin zafin hamada, Amma a haka dakarun suka cigaba da jan su a kasa, Komai rashin tausayin mutum idan yayi arba da halin da kananan yara da mata ke ciki dola ne ya zubar da hawayen tausayi, Domin wasu lokutan idan mutum ya faɗi kasa sai dakarun ya zabga masa wata bulala,yake inda bulalar ta sauka zai fashe jini yayi tsartuwa, Tun kafin a iso kofar birnin waɗansu girɗa girɗan dakaru suka wangame makekiyar kofar birnin, Suna zuwa suka kunna kai izuwa Ciki, Daga ciki birnin yakasance tafkeke na gaban kwatance,gaba gine ginen sa anyi su ne bisa tsari mai ban sha'awa, Duk inda mutum ya kalla jama'a ne nata kai komo suna gudanar da ayyukan na yau da kullum, Haka dai shugabana yesran suka cigaba da tafiya a cikin birnin,duk jama'a suka hango su sai kaga sun tarwatse sun basu hanya Kai tsaye aka shiga izuwa fadar birnin, ita fadar takasance ƙasaitacciya da aka ƙawatata da nau,ikan kayan kawa da alatun jin dadin rayuwar duniya, kai tsayawa musalta tsaruwa da kawatuwar fadar zai iya zama kauyanci sai dai abinda idanu suka gani kawai, A wannan lokaci fadar ta cika maƙil da jama'a maza,mata yara da manya tare da yan majalisa, Zaune abisa wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'anta ta da karfen jauhari aka yi mata feshin ruwan zinare. Wani garjejen mutum ne mai kimanin shekaru talatin ,yana sanye cikin ƙasaitacciyar shiga irin ta hamshakan sarakai, kansa sanye da KAMBUN SARAUTA, Kallo ɗaya zaka yiwa mutum kaji baka marmarin sake haɗa idanu dashi saboda tsananin munin fuskar sa da mai kallo zai yi tsammanin tun fuskar take dariya ko murmushi basu taba wanzuwa akan ta ba. Ba wani bane wannan mutum ba face sarki Uhaisu ibn Falluz....

Available to read on app and web
FATAUCIN BAYI 3

fataucin bayi 3

0 read
0
₦100.00

Kallo ne ya wakana tsakanin kilimat matar wannan mafarauci da ayarin gwaggwan birran na ɗan wani lokaci. Daga can sai birirrikan su kayi wani mahaukacin gurnani mai matukar ban tsoro,wanda ya ɗimauta duk wata halitta dake dajin, bishiyoyi suka dunga rangaji suna karairayewa suna faɗuwa kasa, Wani daga cikin birran wanda alama shi ne shugaban su ya daka musu wata tsawa dake nuna cewa su afkawa kilimat, Ai kuwa su ka yi ɗauki kanta suna masu ɗaya sungumin dake hannun su,suna ihu da kururuwa mai firgitarwa, Shi kuwa shugaban birran sai ya samu wani ɗan faffaɗan dutse ya zauna a kansa yana mai harɗe kafafun sa, yana mai zuba idanu domin ya ga Abin da zai wakana, Koda ganin hakan sai kilimat ta daga takobin ta sama sannan ta ruga izuwa kan birran tana ihu da kururuwa mai firgitarwa ta hausu da sara da suka, Su kuwa birran sai suka shiga kai mata duka da bugu da sungumin su cikin wani irin zafin nama, Duk sa'adda tmda da takobin kilimat ta sari jikin birran sai taji kamar dutse ta sara domin ko gezau basa yi, Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin ta kenan, yazamana ta canza salon fadan ta A inda ta dunga saran su da takobin ta gami amfani da hannun ta ɗayan tana gabza musu naushi da bugu,da dukkan ƙarfin ta, Gaskiyar masu iya magana da suka ce "Idan kiɗa ya canza dola ne rawa ma ta canza,nan fa yazamana cewa kilimat ta fara samun galaba akan birran, domin duk wanda ta gabzawa naushin sai kaji ya tsandara ihu ya ya faɗi kasa yif!. Koda kilimat ta fahimci cewa KARFIN DAMTSE,yafi tasiri akan birran sai kawai tayi jifa da takobin ta Ta shiga amfani da hannayen ta biyu gami da kafafun ta, Duk inda ta sanya a gaba sai dai kaga gawarwakin birran na zube kasa matattu Wohoho! Tabbas karfi da jarumtaka ba,a siyan su da kuɗi face Baiwa da ga Allah, Komai tsakanin hassadar mutum idan yaga yadda kilimat ke ragargazar birirrikan dole ne ya jinjina mata ya san cewa ta ciri tuta a cikin jerin manyan JARUMAN DUNIYA, Nan fa kururuwa gami da hargagin birran ya cika dajin baki daya, jini ya dunga tsartuwa yana kwaranya a kasa, Hakika waɗannan birrai suna ganin tashin hankalin da basu ganin irin sa ba. Kilimat ta zame musu alaƙaƙai, cikin Abin da bai gaza daƙika goma ba ta kashe fiye da kaso biyu cikin uku na birran, Sa,adda shugaban birran yaga irin muguwar barnar da kilimat ke yi masa sai ya cika da matukar mamaki, domin fiye da shekaru ashirin suna zaune a wannan daji basu taba ganin bil'adama da yayi musu barna kamar haka ba, Nan take zuciyarsa ta kama tafarfasa tamkar zata kone, kawai sai ya takarkare ya kurma wawan ihu da sanya bishiyoyi suka dunga karye suna faɗuwa kasa, duwatsu suna karo da juna su na yin bindiga, Kawai sai sauran birran da ke yaƙi da kilimat suka zubar da makaman su suka ruga izuwa bayan bishiyun dake dajin su ka ɓuya, A lokaci guda shugaban birran ya tsuke bakin sa,sannan ya dako wawan tsalle daga kan Dutsen da yake zaune ya durfafi inda kilimat take, Yayin da ya isa gaban ta nan take kilimat ta zamo yar mitsitsiya tamkar an ajiye kyanwa a gaban kare, saboda tsananin tsawo da girman gwaggwan birin, Kafin kilimat ta yi wani yunkuri birin ya shammace ta ya gabza mata wawan naushi a fuska da hannun sa ɗaya, Saboda matukar ƙarfin naushin sai dai kilimat tayi katantanwa a sama sau uku Sannan ta faɗo kasa tim! A matukar galabaice, Cikin karfin hali ta mike tsaye da nufin ta mayar da martani amma sai birin ya cafkota da hannun sa ɗaya ya matse ta ya cika yi mata lugudan naushi a fuska nan take fuskar kilimat ta kumbura, jini da majina su ka yi kaca kaca akan fuskar ta, kuma numfashin ta na fita sama sama ...

Available to read on app and web