Showing 2 of 2 books
Ciki da Gaskiya

ciki da gaskiya

20 reads
5
₦400.00

Falon yayi shiru, kowa ya maida hankalinsa ga baffah, dukda ba wannan ne karon farko da aka ta6a irin wannan taronba agidan kuwa. Amma a wannan karon sai taron yafirgita zuciyar wasu daga cikin al'ummar gidan, musamman ma hajia babba da gwaggo bintu, Dan taron harda su Aysha aciki, da ita kanta gwaggo bintun. Bayan an bud'e taro da addu'oi Ammah tafara magana. Nasan zakuyi mamakin wannan taro, to kudaina mamaki, nice nasaka babanku yayishi, maganar gsky taron yashafi wasunku, kuma ina fata yazama alkairi agaremu baki d'aya. Ta maida kallonta ga baffah, tareda jinjina masa kai, alamar tabar wuk'a da nama a hannunsa. Baffah yafara da sallama da nasiha, sannan yad'ora da fad'in wannan zama yashafi 6angarorine guda biyu zuwa uku. Na farko shine bintu wadda kuke kira Maman yara tanada alak'a ga fad'ima, nasan kuma duk kunsan haka. Duk suka amsa da eh. To alhmdllh, daga yanzun tafita daga jerin masu aikin gidannan, itama tadawo cikinmu, zata cigaba da zama wajen fad'ima insha ALLAH. Kowa ya nuna farincikinsa, Dan bazasu iya manta alkairin gwaggo bintu ba akan d'awauniyar yaran gidan, tundaga kan Amatullah taketa d'awainiya dasu, wannan yasaka taci suna Maman yara. Ayanda nakula hajia babba ce kawai batayi na'am da batunba, amma batace uffanba. Baffah yaciga da fad'in, akwai yarinyar Hama maisuna bishirah, zatayi aure nanda 2 month's idan ALLAH ya kaimu, to tunda bikinta yataho, itama mun dakatar da ita ta huta, ALLAH ya Sanya alkairi. Nanma akace amin. 6angare na biyu kuma shine, za'a kawo sabbin masu aiki su hud'u insha ALLAH, dansu zama canji gasu bintu d'in. Kashi Na uku kuma shine maganar auren Mu'azzam!...... Kowa Afalon saida yad'ago ya kalli baffah, musamman ya khaleel da k'irjinsa yay tsawar hadarin gabas Na tsakkiyar ogusta...

Only available on app verified
Duk inda ta fada

duk inda ta fada

15 reads
0
₦600.00

Riya riya wasu yan mata suka rankayo su ukku da ganinsu kasan talauci ya musu shigar gaske,babu wata me sassauci a cikinsu,ko kallonsu kayi sai sun Baka tausayi domin wannan tana wane wannan a talauci,babu me ran gwame,wani company naga sun shiga da sanyin safiya domin ana fitowa daga Sallah suka fito domin zuwa wannan company, daya daga cikin yan matan tace Ramlat muyi sauri kin San mun makara nasan yanzu wasu tuni sun fara aiki,ke dama Uwar nauyi komai bakyayi da jikinki,Murmushi kawai Ramlat ta saki wanda dimple dinta ya lotsa fararen jerarrun hakoranta suka bayyana, Sannan ta kalli kawar tata tace haba Habiba duk saurin da mukeyi bakya gani,Firdausi tace kyaleta Ramlat iya rabonmu shi zamu samu dai, Firdausi tace iyye to Ku hade min kai yan iska ke Firdausi da kuke hade min kai karki manta Ramlat ita tana da gata a company citta domin kowa Sonta yakeyi har turawa karewa,kalli dai Boss duk girman tumbinsa bashi da buri sai son Ramlat,kowa Ramlat yake so cewar Habiba, Firdausi tace hmm ke dai bari ai ke Ramlat ki godewa Allah ya baki farin jini,duk inda kika shiga sai an soki,da ganinki gaskiya ruwa biyu ce ba yar Asalin Nigeria bace,kina samun Hutu za ayi kallon baiwa sosai. Ramlat dai bata ce komai ba binsu da kallo takeyi tana takunta dai dai cikin birgewa da iya tafiya, Firdausi ta kara magana Habiba bani da Ramlat ba rainin hankali ga isa da takama magana sai taga dama,haka duk mazan dake sonta amma bata taba Kula kowa ba ni anya kuwa baki da Aljanu Ramlat,kiyi aure mana ki huta da wannan wahalar duk fatarki ta dafe,da ace mune da samarinki da tuni munyi aure wlh,mu samu me kudi ko me rufin asiri mu aura duk da karancin shekarunmu kuwa ko dan mu huta da wahalar rayuwa da gararanba a duniya. Har ciki suka shiga suna hirarsu abun mamaki mutane damkam maza da mata Ma'aikata a cikin wannan company,tarin Citta wato Ginger trailers da yawa gasu nan ana juyewa,matan suna zabar Ginger me kyau suna cika buhuna,ga wasu turawa a gefe suna duba aikin,duk wacce tayi buhu daya a bata Dari biyu,haka wasu sai suyi buhu Goma rana daya,wasu buhun Goma sha,babu me kasa da Buhu Goma sai Ramlat kadai,domin Ramlat tsabar lalacinta kullum buhu biyu zuwa uku takeyi watarana ma buhu daya,Mazan kuma suna dinke buhun Citta suna sawa a cikin trailer, company dai na Turawa ne,haka wannan yan mata ma suna shiga suka kwashi buhu suka fara aiki ka in da na in,ba ji ba gani.kafin kace me sunyi furu furu gashin idonsu kamar hazo akayi me yawan gaske, Lokacin Sallah nayi Ramlat ke fara zuwa tayi Alwala sabo da haka suke ce mata agogo domin kowa yana ganin Ramlat ta tafi Alwala yasan time din Sallah yayi,basai sun duba ba kawai zasu kama Alwala maza da mata a hada jam'in sallah ayi, Idan Azahar idan la'asar ma tayi haka, Kowa ya samu kudin aiki zaka ga ana ta siyen abinci ana ci amma banda Ramlat,gashi tana Jin uwar yunwa sai dai tasha ruwan pampo tayi tagumi a gefe tana nazarin duniya. Yauma tana gefe kamar ko yaushe,Firdausi tace Ramlat kiwa kanki fada ki kara dagewa ko buhu Biyar ki dingayi a rana saboda yawan kudinki su Karu ko kya samu ki dinga cin abinci,da ranki da lafiyarki sai banzan lalaci, komai na duniya baza kiyi da jikinki ba,kalli duk mazan gidan nan har turawa masu company sai sun sai miki abinci ayi ta turuwar kawo miki a abinci amma kiki karban na kowa kice baza kici ba,muma mun kawo miki bakya karba,tunda hakane ki kara dagewa da kanki ki samu nacin abinci tun kafin Ulcer tayi miki mummunan Kamu, Haka akayo caaaa kan Ramlat kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Boss ne ya shigo Company da katuwar motarsa ya fito da cikinsa kato,ledojin abinci ne a hannunsa na wani restaurant,Ramlat ya mikawa Leda biyu,ta bishi da kallo tana Murmushi amma bata karba ba, Wato tsohuwa tukuf Binto tace ke yar nan keko ko aljana ce ne yarinya kamar jaraba yanzu da kinso Boss dinnan da tuni bamu washe ba,ke ba yar gidan uban kowa ba sai Mulki da jiji da kai,ke ba yar makaranta ba ba kowan kowa ba amma dan kin samu ana kulaki sai feleke kikeyi, Boss dai baijin hausa,da kyar Ramlat ta karbi abincin tace wa Boss tnx Boss, Murmushi yayi mata ya wuce Office,Binto tsohuwa tace heeeee rai fes ko kefa yarinya inama ni Boss yake so da wlh aurarshi zanyi,can Tsohuwar ta kuma cewa inama ni yayar Boss ce ko yar uwarsa da me zai kawoni aiki gidan Citta, Dariya kowa ya sheke da ita,tsohuwa Binto ta dauko zogalenta da kuli harda tumatur da albasa ta hada abinta taci ta koshi ta Mike taci gaba da aikinta suna ta hira ana kwasar dariya Har Ramlat tana cin dariya. Wata tsohuwa ma ana ce mata Dandubu ta fara magana ke yarinya me farin jini ki auri Boss mana tunda shi musulmi ne,Ramlat ta tabe baki a hankali cikin muryarta siririya me zaki ta furta Allah kiyaye me zanci dashi duk katon ciki, Dandubu ta rike baki dan Ubanki cikin za kici?bafa cikin zaki ci ba,yanzu da kin aure shi Ai da munci gaba,nanma aka sheke da Dariya. Binto tace dan nasan tana aurenshi zai bani Manager,dariya akayi Wasu yan mata suma suka ce Binto ai sai me ilmi ake bawa. Binto dai zazzabi ne ya kamata amma tsabar son kudi taki ta huta,anyi anyi ta huta taki yarda,sai makyarkyata take tana aikinta, Boss ya fito duba aiki yaga Binto tana karkarwa,driver dinsa bakar fata ya kira yana fada masa da turanci shi kuma ya fada musu da Hausa,idan sun fada ya fadawa Boss da turanci. ...

Only available on app verified