Dont trouble till trouble troubles you 

Showing 5 of 14 books
SADAUKI UBAN SADAUKAI 5

sadauki uban sadaukai 5

1 read
0
₦100.00

Yayin da dakaru sukaga abunda sarki ayyub yaiwa sarkinsu sai suka zare takubbansu suna shirin afkama sarki ayyub, sarki ibbahu dake yashe a kasa ya daka masu tsawa sannan yai masu inkiya da su ja su basu guri . Sarki Ayyub ya juyo ya fuskanci sarki ibbahu, shi ko sarki ibbahu sai ya murmushin mugunta ya shafa habar bakinsa inda yaji danshi danshi koda ya duba sai yaga jini, ai nan da nan ransa ya dugunzuma, take ya taso a kan iska tamkar an cilloshi daga cikin baka ya iso gaban sarki ayyub ya gabzamai naushi a baki, ai saboda karfin naushin sai da sarki ayyub yai baya yaje ya gwaru da bangon ginin ya hudata ya fice ya sake huda bango na biyu ya tunkari bango na uku ai koda ya hade da bango na uku sai wata irin sauti ta bayyana sarki ayyub ya fadi a kasa sumamme, . Sarki ibbahu ya bace daga inda yake ya bayyana a kan sarki ayyub yana mai kyalkyale dariya sai da yayi mai isarsa sannan ya budi baki yace wannan shine maganin masu taurin kai da rashin biyayya, Ya daka wa dakarunsa tsawa suka zo sukai kurkuku da sarki Ayyub *** Saida yarima juraish da lubaina suka shafe watanni biyu suna tafiya batare da sun kara gamuwa da wani abun cutarwa ba, sannan suka iso wani kungurmin daji da ake kira da Darul marid, shidai wannan daji na darul marid babu komai a cikinsa face wasu irin jibgagan maridai masu tsananin yawa wayannan maridai kaifin takobi ko tsafi baya tasiri a kansu, hakanne yasa mutane da aljanu suka kauracewa darul marid domin kuwa duk ayarin da maridan sukai arangama da ita cikin kankanin lokaci suke murkushe su, . Dajin darul marid shine hanya mafi sauki da za a isa birnin maharsabar amma saboda wayannan maridan dake rayuwa a dajin ya sanya mutane da aljanu gamida dabbobi suka kauracewa dajin, sau da dama mayaka sunsha yin gangami domin su yaki maridan amma take maridan suke hallakasu, . Koda su yarima suka shigo cikin dajin sai suka tsinkayi bakon yanayi domin kuwa tun shigarsu dajin basui arba da wani abu mai rai ba, hatta bishiyoyin dajin sun bubbushe, cikin tu'ajjibi yarima juraish ya dubi lubaina yace da ita "yake yar uwata Al'amarin wannan daji fa daban mamaki yake Lubaina tace kai kuwa me yabaka mamaki Yarima Yarima juraish juraish yace yace yace gani gani nai nai nai tun tunshigowarmu wannan daji kawo izuwa yanzu banga wata dabba ko kwaro ba hakanan dukkan bishiyoyin dajin ma matattu ne, shin bakya tunanin wani tarkone aka hadamana, lubaina tayi murmushin yadda da kai tace ai koda ma tarkon ne akai mana da yardan ubangiji sai mun tsallake . Suna cikin maganar ne suka ji kasa ta fara girgiza tamkar zata rufta ai nan da nan wasu jibgagan mutane masu tsananin tsayi da girman jiki suka fara futowa ta cikin kasa, yarima da lubaina ko da sukaga haka sai suka ja gefe suna kallon ikon Allah, sai da mutanen su ka gama futowa sannan suka jeru sahu sahu, su dai wayannan halittu ba'a kirasu da mutane ba sai dai Maridai domin kuwa tsayinsu yakai kamu talatin fadinsu kuwa kamu biyar, maridan suna sanyene da wargin fatar dabbobi, suna da sura irin na mutane, shugaban maridan ya daka wa su yarima juraish tsawa yace kai kananun halittu shin wani gangancine ya sanya kuka ratso wannan daji, da alamu dai kun gaji da rayuwa ne shiyasa, shugaban maridan na gama fadin hakan yaiwa sauran maridan tsawa suka afkawa su yarima juraish Ai koda maridan suka afkawa su yarima sai aka kaure da masifaffen yaki,su dai wayannan maridan basa rike da makami faratan hannuwansu suke amfani da shi wurin kaiwa su yarima duka, aduk lokacin da maridi guda yakawo sara yarima ya goce farcen maridin ya dira akasa sai kaga wawakeken rami ya samu, . Yarima da lubaina sai tsalle tsalle da zillewa harin maridan suke yayin da lokaci lokaci su kan kai hari amma koda sun yi nasarar saran maridan ma a banza don takobi baya tasiri a jikinsu , ai koda aka shafe sa'a guda a na wannan artabun sai yarima da lubaina suka fara gajiya, a daidai wannan lokaci ne wani maridi ya shammaci lubaina ya yanketa da farcensa a dantse ai saboda tsananin zafi sai da ta kwala ihu, yarima dake nesa da ita ya rugo ya iso gareta cikin zafin nama ya yaga rigarsa ya daure mata inda taji raunin, . A zucciye ya mike ya kwarara ihu sannan ya sabi ambatan sunayen Allah a zuciyansa, ai nan da nan sai yaji wani sabon karfi ya shigeshi , wani maridi ya wafci lubaina ya daga ta sama yana kokarin wurgata cikin bakinsa, yayinda yarima yaga haka sai ya daka tsalle yai sama ya dira a tsakiyan kan maridin, ya dungula hannu ya gabzawa maridin naushi a tsakiyar ka ai saboda karfin naushin saida tsakiyan kan maridin ta fashe fus tamkar an fasa kwakwa, maridin ya saki ihu kana ya fadi a kasa matacce . Yayinda sauran maridan suka ga haka sai suka harzuka nan da nan suka afkawa su yarima aka fara sabon artabu inda yarima da lubaina suka kasance tamkar aljanu a tsakiyan maridan domin kuwa sai zubar da su suke tamkar ana sassabe a gona, Sai da suka shafe sa'a biyu suna wannan artabun sannan yarima juraish da lubaina suka samu nasarar karar da maridan gaba daya, sai a wannan lokacin suka lura da raunikan da maridan suka ji masu, batare da bata lokaci ba suka shafa magani a raunukan sannan suka yada zango a cikin dajin , Kashe gari da sasssafe sukai shiri suka tunkari birnin maharsabar, tafiyar kwanaki biyarce ta kaisu ga birnin yayin da suka iso bakin kofan birnin sai dakarun dake tsaron suka daka musu tsawa suna tambayarsu ko su su waye, Yarima juraish ya budi baki yace Mune guguwar Annoba ma'abota kawar da zalunci, kui sani cewa ba komai bane ya kawo mu wannan birni naku ba face mu durkusar da mulkin zaluncin sarkinku sannan mu kafa daular Musulunci Koda dakarun dake tsaron kofa suka ji haka sai suka bushe da dariya, Haka sukaita kyalkyalar dariya kafin shugaban dakarun ya daka wa yarima tsawa yace "kai yara da alama kun gaji da duniyarce, to ku sani cewa kunyi kadan da kuyi mana juyin mulki cikin alfamar da zamu iya maku shine ku juya ku koma inda kuka fito tun kafin ku fusata mu aikaku lahira, Wani badakare daga cikin dakarun ya matso kusa da shugaban kofa ya dafa kafadarsa yace haba ya sarkin kofa ya zakace su koma bakaganin waccan kyakkyawar budurwar sai kumbura take ba, yana gama fadin hakan suka sake bushewa da dariya a karo na biyu, Zuwa cab sarkin kofa yace ke baa ...

Available to read on app and web
SADAUKI UBAN SADAUKAI 4

sadauki uban sadaukai 4

1 read
0
₦100.00

A rayuwar sarki ibbahu babu abunda yafi kauna kaman dansa yarima dumakisu , yana matukar sonsa,baya kaunar duk wani abun da zai cutar dashi, _ Sarki ibbahu ya shiga cikin wani turaka inda ya iske yarima dumakisu a kwance akan katifa shida wata tsaleliyar yarinya suna aikata alfasha, yayinda yarinyar ta dago kai tai arba da sarki ai sai ta rude, cikin firgici ta mike ta saka kayanta ta fice daga cikin turakar a guje, sam wannan abu bai baiwa sarki ibbahu mahaifin yarima dumakisu mamaki ba dun sabon abu bane a wurinsa, . Yarima ya dago kai ahankali ya dubi mahaifinnasa yace "ya abbana shin meya farune daka zo ka gintse mani jindadina" Sarki yace "ka shirya yanzu ka sameni a filin koyon yaki"yana fadan haka ya fice daga dakin, Cikin kasala yarima dumakisu ya mike ya fara shiryawa, cikin kankanin lokaci ya fito cikin shigar sarauta, Yarima dumakisu lafcecen katone sai de bai kai sarki ibbahu girman jiki ba, yana da doguwan fuska,mai dauke da dagwa dagwan idanuwa da shirgegen karan hanci, gamida tsukakken baki, ba karamin kama yake da mahaifinsa ba, ...

Available to read on app and web
SADAUKI UBAN SADAUKAI 3

sadauki uban sadaukai 3

2 reads
0
₦100.00

Rundunar Gwaggon birin suka cigaba da tafiya har suka iso sansaninsu inda gidajensu yake, gwaggon daya dauko su yarima ya sarkafesu a saman wani itace, gaba dayan gwaggon birin suka wuce gidajensu da suka sana'anta da bishiyu, . Kashe gari da safe wani gwaggo yazo wurin su yarima yana zuwa ya daukesu ya nufi wani babban gida da su, Shidai wannan gida yafi kowanne gida girma da tsaruwa a sansanin gwaggon birin, gwaggon na isowa bakin kofan gidan ya watsa su yarima juraish cikin gidan sannan yai wucewarsa . Koda Yarima juraish da lubaina suka tsinci kansu a cikin gidan daya kasance mai matukar duhu sai suka fara Addu'a a zukatansu Ba zato ba tsammani sai sukaji gurnani na tashi a bayansu, sukai kokarin juyawa amma suka gagara saboda daurin da ragar tai musu, haka dai gurnanin yacigaba da tashi lokaci guda gurnanin ya dauke diff sannan haske ya gauraye gidan da suke ciki, . A kokarin da su yarima suke na ganin sun juyo ne suka gungure akas inda sukai arba da abun da ke gurnanin Wani irin gwaggon birine mai girman gaske, domin girmansa ya ninka na yan'uwansa sau uku, gwaggon birin ya mika hannunsa ya dauko su yarima juraish tamkar ya dau ya yan kaji sai da gwaggon ya gama kare masu kallo sannan yayi watsi da su suka bugu da gini, gwaggon ya sake daukansu ya duba ko haryanzu suna raye, ashe lokacin dayai watsi da su suka gwaru da gini lubaina ta suma sakamakon buguwan da kanta yayi, koda gwaggon birin yaga lubaina bata motsi sai ya saka farcensa ya barke ragar daya dauresu yarima ya fiddo da lubaina yana kokarin kaita bakinsa . Ai koda yarima juraish ya ga abun da gwaggon ke shirin aikatawa sai ya zare takobinsa ya kurma ihu, ya fara sukan jikin gwaggon birin tamkar yana sukan buhun hatsi, duk inda ya soka da takobinsa sai kaga takobin ta shige ciki haka zai zarota jini yai feshi amma shi gwaggon birin bai ma san yana yi ba . A yayin da gwaggon birin ke kokarin handama lubaina a bakinsa ne yaji kyaikyayi-kyaikyayi a kafarsa ta hagu hakan yasa ya dubi kafan nan take yai arba da yarima juraish sai soka wa kafar takobi yake yana zarewa , a matukar fusace gwaggon birin ya mika hannunsa ya dauko yarima juraish tamkar ya dau fallen takarda , yayin da yarima juraish ya tsinci kansa a hannun gwaggon birin sai ya kama wutsistsila kafafuwa yana neman kwacewa, batare da bata lokaci ba gwaggon birin ya wurgasa cikin bakinsa da nufin yai masa tauna daya, sai de kash rashin sani yafi dare duhu, da ace gwaggon birinnan yasan abun da zai biyo baya da baiyi gangancin wurga yarima juraish cikin bakinsa ba, . Yarima juraish na fadawa cikin bakin gwaggon birin, sai ya kasance tamkar gugace ta fada rijiya,zakwa zakwan hakwaran gwaggon birin suka fara motsi na sama suka fara yowa kasa, na kasa suka fara yin sama, koda yarima juraish yaga haka batare da bata lokaci ba ya hau sara da sukan gaggwon birin ta ko'ina a bakinsa, Gwaggon birin ya kurma ihu sakamakon zafin daya ji a bakinsa ya sanya hannu cikin bakin yana kokarin fiddo da yarima juraish, . Yarima ya falfala da azababben gudu ya haye saman hannun gwaggon birin ya daka tsalle ya dira a saman hancinsa, yana dira ya cigaba da sara da sukan kogon hancin , gwaggon birin ya kurma uban ihu ya fadi a kas yana kokarin mikewa ne yarima ya haura saman idanunsa ya daga takobinsa ya caka a kwayar idon gwaggon birin na dama, gwaggon birin ya sake rafka wata ihun mai tsananin firgitarwa . Nan take ya fara rarume rarume , yana doke doke, duk wannan abu dake faruwa lubaina na some a hannun gwaggon birin, yarima juraish ya sake caka wa gwaggon birin takobi a kwayar idon sa ta dama, . Da gudu gwaggon birin ya futo daga cikin gidan da yake yana mai kurma uban ihu, nan ya hau kai duka yana kwala ihu a duk sa'in da hannunsa yayi nasarar damkar bishiya komai girmanta sai de kaga ya tunbuketa yai jifa da ita, . A wannan lokaci yan uwan gwaggon birin sun fita farautar wani naman, akullum haka gwaggon birin suke dazarar sun kamo nama sai su kawo wa shugabansu sannnan su sake komawa farautar wani naman, Yayin da gwaggon birin ya fito sansaninsu yana ihu gamida buge buge, wani irin bakin ruwa na ficewa daga idanuwansa, har a wannan lokaci lubaina na some a hannunsa, koda ruwan idon nasa ya fara gangarowa sai ya diga ajikin lubaina, a firgice ta farka tana kwala kabbara, . Yarima juraish ko sai ya falfala da azababben gudu har ya wuce gwaggon birin ya yanki daji koda yai nesa sai ya tsaya a wani wuri ya kwala wa gwaggon birin kira, ai nan take sai gwaggon birin ya dumfaro inda yaji sautin muryan yarima, yana isowa wurin yarima ya yanke wata igiyar kalgo, take wata damfa reriyar itace mai kauri da tsayi tai fitar burgu daga bayan yarima ta dumfari gwaggon birinnan, itacen ta doki gwaggon birin a fuska, ya fadi gefe guda, Yarima juraish ya falfala da gudu ya haye kan gwaggon itama lubaina ta falfala da gudu ta haye kan gwaggojn birin kafin gwaggon ya farka tuni har yarima juraish da lubaina sun daka tsalle sama suna masu kurma ihu, suka dira a cikin idanun gwaggon birin da takobinsu, take takubbansu suka lume a kwayan idanun, wani irin bakin ruwa ya fara fitowa daga idanun gwaggon yana bin kumatunsa, gwaggon birin ya kurma azababbiyar ihu ya murgina kasa matacce, . Yarima juraish ya zaro takobinsa daga kwayar idon gwaggon ya maida cikin kubenta ya mika wa lubaina hannu ta mike tsaye, a lokaci guda suka daka tsalle daga kan gwaggon birin cikin gwaninta suka dira a akan turba, . Batare da bata lokaci ba suka fara tafiya, yayin da suke tafiyarne lubaina ta fuskanci yarima juraish ba cikin hayyacinsa yake ba ganin suna tafiya yana tangal tangal, hakan yasa ta matso kusa da shi tana kokarin ta tallafoshi, a lokacinne yarima juraish ya tsaya cak a wuri guda idanuwansa suka fara lumshewa,take ya fadi akasa jigim . Da sauri lubaina ta dago shi zaune koda ta tallafo wuyansa sai taga jini na bulbulowa daga gefen wuyansa, ashe yayin da yake artabo da gwaggon birinnan ya yankesa da farce, Cikin gaggawa lubaina ta sanya mai magani a raunin ta kwantar da shi a gefe guda don ya huta, __ Al'amarin rundunar gwaggon biri kuwa koda suka fita farauta basu da dawowa ba sai yamma, inda sukai arba da gawan shugabansu, koda sukaga haka sai dukkansu suka kwala ihu suna wani irin gurnani wanda ya karade dajin baki daya, ba shiri tsuntsaye da kananun halittu suka fara kaura suna canja matsuguni, Ba shiri gwaggon birin suka bazama cikin dajin suna masu falfala uban gudu, inda komai girman bishiya da zarar sun hadu da ita sai kaga ta tumbuke tayi gefe . Al'amarin yarima juraish kuwa koda ya dan samu hutu sai ya farka cikin kuzarinsa tamkar babu wani abun daya sameshi ya dubi lubaina yace maza ki shirya mu kara gaba domin kuwa bamu ga ta zama ba, muddin gwaggon birinnan suka dawo sansaninsu suka tarar mun kashe musu dan'uwa tofa sai sun bazama nemanmu . Lubaina tace ai babu fa'idar guduwa masu alhalin duk gudunmu sai sun cimmana mun gwabza yaki da su, gwara muyi zamammu anan su zo su samemu tunda sai mun hallakasu sannan zamu saman daman ketare wannan daji Yayin da yarima juraish yaji haka sai ya koma ya zauna yace maganarki dutse amma fa kisani masu iya magana sukace ja da baya ga raggo ba tsoro bane... Ai yarima bai gama rufe bakinsa ba suka farajin karar karairayewan bishiyu da gurnanin gwaggon birinnan, kafin kace kwabo har rundunar gwaggon birin nan sunyiwa su yarima kawanya ,lokaci guda yarima da lubaina suka zare takubbansu kana sukai kabbara suka durfafi rundunar gwaggon birin, Gwaggon birin sukai kara gamida dukan kirjinsu suma suka nufo kan su yarima, koda rundunar gwaggon birin da su yarima juraish suka hadu sai yarima da lubaina suka daka uban tsalle suka dira asaman kan gwaggo daya, lubaina ta dira a gefen idon hagun gwaggon yayin da yarima ya dira a gefen idon damansa, lokaci guda suka daga makamansu suka soke idanuwan gwaggon, gwaggon ya kwarma ihu ya fadi a kasa matacce , yayinda yan uwansa sukaga haka sai suka kara fusata sukayo kan yarima da lubaina tamkar zasu cinyesu danye...

Available to read on app and web
SADAUKI UBAN SADAUKAI 2

sadauki uban sadaukai 2

0 read
0
₦100.00

Suna kokarin bude kofan kenan kwatsam sai wata zazzakar murya ta bayyana tana mai kyalkyalewa da dariya, dukkansu suka juyo don ganin me muryar,anan sukai arba da wata kyakkyawar budurwa tana kyalkyale dariya . Ita dai wannan budurwa tana zaune ne akan wani kasaitaccen karagar mulki da'aka sana'anta da zallan yakutu, budurwar na sanye da doguwar rigan alhariri an yiwa rigar cinbaki da lu'u lu'u ya rigar dame jikinta ta yadda ya bayyana dukkan wasu surorin jikinta, . Yarima juraish ya saki baki yana kallon budurwan tun da yake a rayuwarsa bai taba ganin mace mai tsananin kyawu ba kamar wannan budurwa, hatta lubaina datai arba da budurwar sai da kishi ya kamata na ganin ta dareta kyawu nisa ba kusa ba, Budurwar ta tsaida dariyar nata lokaci guda ta turbune fuska, in kaganta sai ka rantse ba itace ta gama kyalkyalar dariya ba . Budurwar ta nuno su yarima da hannu tace "yaku wayannan mace dana miji ina mai yi maku lale marhabun da zuwa Gabatul maut, Dajin mutuwa, dajin da duk abun da ya shigo baya fita, lallai kusani kun aikata mummunan kuskure arayuwarku na shigowa cikin dajinnan," Yarima juraish ya ce da budurwar a fusace "yake wannan kyakkyawar budurwa,kiyi sani cewa mu matafiyane hanyace ta biyo damu ta cikin dajinnan, izan har ya kasance mun aikata wani laifi ne agareki na shigowa dajin to muna mai baki hakuri,batun zaki hallakamu kuwa sam bai taso ba" . Koda budurwan taji haka sai ta kara daure fuska tamau tace "nasan baku san koni wacece ba shiyasa, to kusani nice sarauniya Murkisa mai mulkar birnin DUMA, na kasance ne a cikin dajinnan don aiwatar da wani babban sihiri wanda muddin na kammalashi zan zamo gagarabadau ga sauran sarakunan duniya, kasata zata bunkasa a fannin tattalin arziki, shekarata hamsin cikin dajinnan ina kokarin hada sihirin, ta hanyar zubda jinin duk wani bil'adama ko aljanin daya ratso ta cikin dajinnan, na hallaka bil'adama da aljan dubu casa'in da takwas, saura mutum biyu ya rage na kammala sana'anta sihirin inda zan zamto gagarabaudau din sarauniya, ina mai umartarku da ku kashe kawunanku da kanku tun kafin kaifin takobina ya ratsa girazanku" Sarauniya murkisa ta idda maganarta cikin tsawa da gargadi . Azucciye yarima juraish da lubaina suka zare takubbansu juraish yace "yake sarauniya murkisa zan baki wata garabasa muddin kin yadda da kanki to ki tunkareni muyi bata kashi izan har kika samu nasarar taba jikina ko takobinki ya yankeni to da kaina zan hallaka kaina kana na hallaka yar uwata lubaina, don haka ga fili ga mai doki me yarage" . Koda sarauniya murkisa taji haka sai ta bushe da dariya tace "kasani yakai jarumi juraish kafin ka kagai ga fafatawa dani dole sai ka wuce wasu matakai, " tana gama fadin hakan tafa hannunta tana fadin wasu dalasiman tsafi, nan take dakin ya kama girgiza tamkar zai kife abubuwan dake dakin suka fara tangal tangal kwatsam sai wasu irin dodanni masu munin halitta suka fara fitowa ta karkashin kasa, wayannan dodanni sun kasance jibgaga domin kuwa dodo daya daga cikinsu zai iya cafke mutane uku a hannunsa, dodannin na dauke da kwayar idanu guda daya a akan fuskarsu sai wagegen baki mai dauke da bakaken hakora, babu makami a hannun dodannin, nan fa dodannin sukai kururuwa suka afkawa su yarima juraish da budurwa lubaina . Koda su yarima juraish sukaga haka sai suka falfala da azababben gudu suka tari dodannin koda suka hadu sai suka kacame da bakin gumurzu,yarima juraish da lubaina suka wanzu suna ragargazar dodannin babu kakkautawa,hoho izan da ace mutum na wurin yana kallon wannan gumurzu to da sai yayi zaton yarima juraish da lubaina ba mutane bane, sarauniya murkisa dake zaune akan karaga sai bata rai take na ganin irin yadda yarima juraish ke ragargazar dodanninta, . Sai da aka dau tsawon lokaci yarima juraish da lubaina suna ragargazar dodannin tamkar suna sassabe a gona, duk inda suka sa gaba sai de kaga sassan jikin dodanni na yawo a iska, kafin su samu nasarar hallaka dodannin gaba daya, Yarima juraish ya sanya hannu yana share bakin jinin dake jikin takobinsa ya ce da sarauniya murkisa "ina bai baki shawara da ki gaggauta neman inda dare yai maki kafin kaifin takobina ya iso gareki" Sarauniya murkisa na jin haka ta sake bushewa da dariya a karo na biyu, ta ce "adadin dodonninnan sun kai dubu biyu amma cikin kankanin lokaci kuka gama da su, najin jina ma sadaukantakarku, muje mataki na biyu" sarauniya murkisa na gama fadin hakan ta tafa hannayenta ta na fadar dalasiman tsafi, . Koda ta fara furta dalasiman nan sai yarima juraish da lubaina suka tsinci kansu a tsakiyan daji, cikin mamaki suka dubi junansu daga sama sukaji muryan sarauniya murkisa tana cewa dasu "wannan shine Duniyar gwaggon birrai, babu mutum ko aljan dake rayuwa anan, muddin kuka samu nasarar ficewa daga duniyar nan a raye to zaku cimmini a fadata ta birnin DUMA" muryan na zuwa nan ya dauke dif tamkar bai taba wanzuwa ba,...

Available to read on app and web