Showing 5 of 16 books
ALKALAMIN KADDARA 2

alkalamin kaddara 2

22 reads
0
₦350.00

CIGABAN LITTAFI NA DAYA...

Available to read on app and web
ASABE REZA

asabe reza

0 read
0
₦500.00

Kwallina!' Zuciyarta ta buga da wannan kalmar, jan jikinta ta fara yi tana son isa inda ta jefar da kwallin, ji take shi kaɗai ne Zai iya taimakonta, shi kaɗai ne zai iya hana HAMOUD aikata duk wani abu da yake hari. Dafe kwalbar kwallin ta yi tana ƙoƙarin ɗauka. Da shi da gabjejen takalmin ƙafarsa ya ɗora a hannun nata, ya murje, ya muttsike, ya ƙara murjewa har sai da sautin rugurgujewar kwalbar da yatsunta ya fita, ta kwalla gigitacciyar ƙara jin kwalaben sun lume a tafin hannunta, a haka ta ji sautinsa yana faɗa mata abin da ya dakatar da fitar numfashinta. "Idan akwai halittar da ba zan taɓa yafewa a duka duniyata ta ba, to ke ce Fakriyya. Ki yi zina da mahaifina, ki keta alfarmar mahaifiyata, ki zo kuma ki aure Ni? Wane irin kwamcala ce wannan? Ki faɗa mini me na miki a rayuwa da za ki min wannan hukuncin? Ta ya ya ma na aure ki, me ya sa na so ki? Me zan miki?... Lura: (Akwai tarin sarƙaƙiya a labarin, ku taho a sannu, kuna kiyaye duk wani motsi na jaruman)...

Available to read on app and web
BA GIRIN GIRIN BA

ba girin girin ba

3 reads
0
₦500.00

Burin dukkan iyaye shi ne su aurar da ya'yansu da sun taka munzalin aure musamman ya'ya mata. Hakan ya kasance daga cikin Addini da Al'adunmu. Rashin aure kan haifar da damuwa a zukatan iyaye da su kan su ya'yan amma kamar yanda addini ya koyar da mu cewa "Komai da lokacin sa" shi ma auren ya shiga sahun "komai" ɗin. Gaggawa da kwallafa ran akan sai anyi aure ya sa da yawa daga cikin jinsinmu yin KUSKUREN da har su mutu suna nadamar sa. Jinkiri kan sa mutane su rasa tauhidinsu na duk abin da zai faru a doron kasa ya kan faru ne a bisa ga ikon Allah, in bai so ba hakan ba zai faru ba, kuma komai rubutacce ne, kuma alkaluma sun bushe. Sai su zama su na takurawa wanda aurensu ya zo da jinkiri da kalaman "Yaushe za ki yi aure?" ko kuma "Kin ki aure ko" abin tambaya ga duk wanda ya ke ɗaukan aure a wani hanyar nuna Darajan mutum shi ne "mai ya hana musu mutuwa" don kuwa aure, haihuwa da mutuwa lokutansu rantsattse ne. Babu abin takaici kamar a ce mace don ba ta yi aure ba, sai ma su kiran ta ki aure su zagayo suna neman ta da lalata don a ganinsu tun da ta ki aure toh mazinaciya ce. Wacce gaggawa ya dibe ta sai ta ba da kai bori ya hau don a tunanin ta hakan zai sa su aureta. Wasu daga cikin kawayensu kuma kan ɗauki rashin aure dalilin yanke zumunci da su, saboda a ganinsu babu kaskanci kamar rashin aure ko da kuwa auren da za'a rike zai kai su ga wuta ne ba Aljannar da kowa ke yin aure don nemansa ba. Tsabagen son aure ya sa tun yarinya na kwailar ta ake dasa mata ra'ayin duk abin da za ta yi don farin cikin wani ɗa namiji ne ba wai don kanta ko farin cikin mahallicinta ba. Sai ka ga don yarinya ta ci kwalliya ba za'a nuna mata tayi kyau don ta ji daɗi ba sai dai a nuna mata tayi kyau za ta burge wani ɗa namiji. A haka za ta taso in ba'a taki sa'a ba sai ta kai ga siyar da mutuncin ta duk don ta birge namiji....

Available to read on app and web
SILAR AJALI

silar ajali

5 reads
0
₦500.00

Duk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani matashi dake kauyen da makwabtan kauyukan sun shaidata ne a matsayin daliba mai zuwa makarantar boko. Iyayenta basu da kudi, basu mallaki komai ba sai ita da kanwarta AMINA, daga su sai gatarin faskaren da mahafinta malam TANKO ya gada a wurin kawunsa, daga nan sai tukunyar da Rahanatu ta sani da ake dora musu abinci ba kullum ba. Kullum bata manta maganar babanta "karatun ki shine hanyar ceton mu, ke kamar gona ce da muke shuka muke fatan girban albarkacin noman mu anan gaba, karatun ki ne zai sa mu san dadin cire kudi mu biyawa kanmu bukata, karatun kine zai sa wata rana mu daina lissafa abincin da muke ci, karatun ki ne zaisa wata rana mu iya siyan sutura har mu manta adadin wadda muka mallaka, karatun kine zaisa a rika tunawa damu a matsayin masu rufin asiri. Dan haka kada kiyi wasa da karatun ki rahanatu" ba zata yi ba, saboda tana so taga iyayenta sun fita daga talauci. Ta sha alwashin haka. Sai dai a hanyar ta ta zuwa makarantar taci karo da shaidanin yaro HADI ALJAN. Yaron sarkin garin, yaci alwashin lalata rayuwarta koda ta hanyar fyade ne, bata bashi goyon baya ba, amma kuma ba zata iya hana shi ba Ba zata fadawa iyayenta ba saboda kada hankalinsu ya tashi Kota fada musu ba zasu iya komai ba babansa ne sarki. Ba zata kuma daina zuwa makaranta ba saboda canne fatansu yake. Ba zata iya salwantar da rayuwarta ta yarda dashi ba dan zai lalata rayuwarta. A haka ba yadda zata iya, yayi mata fyade. Ba zata iya fadawa iyayenta ba, duk da saida ta wuni a cikin gona cikin jinni, aka samu mai taimaka mata ta ceceta. Cikin da ya bayyana a jikin rahana shine ya zama silar tarwatsewar iyayenta da ita. Har ta tsinci kanta a birni.... A cikin tarragon rayuwa mai tsananin daci da burin daukar fansa......

Available to read on app and web
ALKALAMIN KADDARA 1 complete

alkalamin kaddara 1 complete

28 reads
0
₦500.00

Karka nuna dan yatsa akan kalar rubutun da Alkalamin kaddara yaima waninka. Baya tsallake kowa, naka a rubuce yake tun kamun samuwarka. Karkace zakai dariya akan kalar shafin rubutun Alkalamin kaddarar wani, a duk minti daya na rayuwarka sabon shafi yake budewa, waya san ko cikin shafukanka akwai rubutun dayafi nashi muni. Karka saki jiki da yawa, komai zai iya canzawa. Zuwa yanzun kowa yasan ban yarda da Happily ever after ba, idan har shi kake buqata, ALKALAMIN KADDARA ba littafin ka bane ba. Yan gidan Tafeeda da Shettima zasu taba rayuwarku kaman yanda suka taba tawa. Bance akwai sauqi a cikin tasu tafiyar ba. Banda tabbas akan abubuwan da zakuci karo dashi in kuka biyoni a wannan tafiyar. Tabbaci daya nake dashi, ba zaku taba dana sani ba IN SHA ALLAH. #AnaTare #VOA #FWA #TeamAK...

Available to read on app and web